Neja: Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Tura Sako
- An shiga jimami bayan rasuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar Neja, Kwamred Muhammad Adam Erena
- Marigayin kafin rasuwarsa shi ne hadimin gwamnan jihar, Umar Bago ta bangaren da ya shafi kwadago a jihar
- Gwamna Umar Bago ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya yi addu'ar samun rahama da gidan aljanna
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Niger - Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya tura sakon jaje bayan rasuwar hadiminsa, Kwamred Muhammad Adam Erena.
Gwamnan ya bayyana mutuwar Erena wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar ne a matsayin babban rashi ga jihar.
Wasu mukamai marigayin ya riƙe a Neja?
Marigayin ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar ne a mulkin marigayi tsohon gwamna, Abdulkadir Kure.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwar marigayin, shi ne hadimin gwamnan a bangaren da ya shafi ma'aikata da Kwadago.
Ya kuma rike shugaban kungiyar ciyamomin NLC na jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya gaba daya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim ya sanar a shafin Facebook.
Gwamnan Neja ya yi alhini kan rasuwar
Gwamna ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙwazo wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin ci gaban jihar.
Ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin inda ya ce dole su yi hakuri da hukuncin ubangiji wanda babu wanda ya isa ya yi tambaya kan haka.
Bago ya kuma roki Ubangiji ya yi masa rahama ya kuma saka masa da gidan aljannar firdausi.
Tuni aka gudanar da sallar jana'izarsa inda mataimakin gwamnan jihar, Kwamred Yakubu Garba da sakataren gwamnatin, Abubakar Usman suka halarta.
Shehun Borno ya tafka babban rashi
Kun ji cewa An shiga jimami bayan sanar da rasuwar babban ɗan marigayi Shehun Borno, Shehu Mustapha Umar El-Kanemi.
Marigayin Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi ya rasu ne a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu bayan fama da jinya a jihar Borno.
Tuni aka yi sallar jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar a yau Lahadi 28 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:00.
Asali: Legit.ng