"Ka Shirya Fafatawa da Ni": Kwamishinan 'Yan Sanda Ya Kalubalanci Dangote Bayan Ya Yi Ritaya
- Yayin da kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra ya yi ritaya, ya sha alwashin gogayya da attajiri Aliko Dangote a harkokin kasuwanci
- Aderemi Adeoye wanda ya yi bankwana da aiki ya bayyana yadda ya tsunduma harkokin kasuwanci tun a shekarar 2018
- Aderemi ya ce sun fara kamfanin zuba hannun jari da N54m inda yanzu suna da ya kai N20bn yayin da ya kalubalanci Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Anambra - Kwamishin 'yan sanda a jihar Anambra, Aderemi Adeoye ya yi ritaya daga aiki.
Aderemi ya ce yayin da ya ke aiki ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci na biliyoyin naira.
Alwashin dan sandan ga Aliko Dangote
Ya sha alwashin fafatawa da attajirin Nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote a harkokin kasuwanci, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya bayyana haka a jiya Asabar 27 ga watan Afrilu yayin bikin barinsa aiki a hedkwatar hukumar da ke birnin Awka.
Adeoye ya ce tuni ya riga ya shiryawa rayuwa bayan aikin gwamnati inda ya ce ya tsunduma harkokin kasuwanci saboda inganta rayuwarsa.
Ya ce a 2018 ya kirkiri kamfanin zuba hannun jari na Alpha Trust Investment Club da N54m amma yanzu suna juya ya kai N20bn, cewar rahoton Arise News.
Ya kalubanci Dangote a harkokin kasuwanci
"Mun dade muna inganta kamfanin wurin saka makudan kudi, a nan da shekaru 10 za mu iya fafatawa da Aliko Dangote har ma mu zarta shi shura."
- Aderemi Adeoye
Kwamishinan ya kuma yabawa rundunar 'yan sanda da kuma al'ummar Najeriya baki daya kan irin hadin kai da suke basu a ƙasar.
Dangote ya rage farashin dizal
A wani labarin, kun ji cewa Matatar man Aliko Dangote ta sanar da rage farashin litar dizal domin samar da sauki ga 'yan kasa.
Matatar ta rage farashin ne daga N1,200 zuwa N1,000 Wanda shi ne karo na biyu da ta ke rage farashin a wannan shekara.
Shugaba Bola Tinubu ya yabawa attajirin kan irin wannan taimako da ya yi inda ya ce hakan zai kara rage farashin kayayyaki a Najeriya.
Asali: Legit.ng