Buhari Ya Yi Ta'aziyya Yayin da Tsohon Sanata da Ɗan Uwan Tsohon Hadiminsa Suka Rasu a Kano

Buhari Ya Yi Ta'aziyya Yayin da Tsohon Sanata da Ɗan Uwan Tsohon Hadiminsa Suka Rasu a Kano

  • Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen ɗan jaridar nan Sidi Hamid Ali, wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Alhamis a Kano
  • Tsohon shugaban kasar ya kuma aike da saƙon ta'aziyya ga tsohon hadiminsa, Abdulrahaman Baffa bisa rasuwar yayansa, Hafiz Baffa Yola
  • Buhari ya kuma yi addu'ar Allah ya jiƙan mamatan ya kuma yafe masu kura-kuransu, ya ba iyalansu haƙuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Daura, Katsina - Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar sanatan jamhuriya ta biyu kuma dattijon ƙasa, Sidi Hamid Ali.

Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Sidi Ali ya rasu ne da yammacin ranar Alhamis bayan fama da jinya a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

Muhammadu Buhari.
Buhari ya aike da sakon ta'aziyya na rasuwar Sidi Ali da Baffa Yola Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Da yake alhinin wannan rashi, Buhari ya bayyana fitaccen ɗan jaridar a matsayin ƙwararren marubuci wanda ya ba da gudummuwa mai yawa, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan da kakakin tsohon shugaban ƙasa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce marigayin ya samu farin jini a lokacin da rubuta littafi kan tagwayen laifuka biyu, cin hanci da rashin ladabi.

"Na yi jimamin rasuwar babban ɗan jarida, marubuci, kuma ɗan siyasa, Sidi H. Ali wanda ya shiga zuciyata da ta mutane da yawa saboda rubuce-rubucensa da littafi biyu da ya rubuta a kaina.
"Ya kasance marubuci mai kirkirar abu da kansa, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalansa da sauran masu fatan alheri."

- Muhammadu Buhari.

Buhari ya jajanta rasuwa Hafiz Baffa

A wani sakon ta'aziyya na daban ga tsohon mataimakinsa na musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa, Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar shahararren likitan nan, Dakta Hafiz Baffa Yola.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata Kuma Dattijon Ƙasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Kano

A cikin sakon da ya aike wa Abdulrahman Baffa Yola, kanin marigayin, tsohon shugaban kasar ya ce Dr. Baffa ya rayu ba don kansa ba sai don iyali, al’ummar Kano da kasa baki daya.

Buhari ya yi addu'ar Allah ya gafartawa mamacin ya masa rahama, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

An hana zirga-zirga a Oyo

A wani rahoton kuma yayin da ake shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi, gwamnatin Oyo ta taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Jumu'a, gwamnatin karkashin Gwamna Makinde ta ce dokar za ta yi aiki daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262