Matar Ministan Tinubu Ta Shiga Jerin Alkalai 22 da Za a Ƙarawa Girma, Akwai 'Yan Arewa

Matar Ministan Tinubu Ta Shiga Jerin Alkalai 22 da Za a Ƙarawa Girma, Akwai 'Yan Arewa

  • Mai dakin Ministan Abuja, Nyesom Wike ta samu shiga jerin alkalan da aka tura kotun daukaka kara domin kara musu girma
  • Eberechi Wike ta kasance daya daga cikin alkalan guda 22 da aka tantance domin tura sunayen nasu kotun daukaka kara
  • Shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola shi ya amince da tura sunayen daga cikin guda 92 da aka tantance

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola ya amince da alkalai 22 da za a karawa girma zuwa kotun daukaka kara.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa inda Ariwoola ya ce shugabar kotun, Monica Dongban-Mensem ta tura sunayen alkalan 92 ga hukumar shari'a ta FJSC.

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

Mai dakin Ministan Tinubu ta samu karin girma zuwa kotun daukaka kara
Matar Ministan Abuja, Nyesom Wike ta samu karin girma zuwa kotun daukaka kara. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Sunaye nawa aka ware domin karin girma?

Daga cikin sunayen 92, guda 22 sun samu damar tsallakawa domin samun karin girma zuwa kotun daukaka kara, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikinsu akwai matar Ministan Abuja, Nyesom Wike wacce ta samu damar tsallake tantancewar.

Eberechi Wike ta kasance kwararriyar lauya wacce ta ba da gudunmawa mai tsoka a bangaren shari'a, Cewar rahoton Tori News.

Wadanda suka shiga jerin alkalan a Najeriya

Wadanda suka samu shiga daga Arewa maso Yamma sun hada da Ishaq Mohammed Sani (Kaduna) da Zainab Bage Abubakar (Kebbi) da Abdulaziz M. Ankara (Zamfara).

Sai Arewa ta Tsakiya akwai Polycarp Tema Kwahar (Benue) da Ruqayat Ayoola da Eneche Eleojo (Kogi) da Asmara Akanbi Yusuf (Kwara) da Abdullahi Muhammad Liman (Nasarawa) da Abdu Dogo (Abuja).

Yayin da Arewa maso Gabas ke da mutum daya kacal daga cikin alkalan wanda ya fito daga jihar Borno, Fadahu Umaru.

Kara karanta wannan

EFCC ta 'gano' asusun da Sambo Dasuki ya tura kudin makamai

A Kudu maso Gabashi akwai Nnamdi Okwy Dimga Victoria (Abia) da Toochukwu Nwoye (Anambra) da Henry Aja-Onu Njoku (Ebonyi) da Donatus Uwaezuoke Okorowo (Enugu) da Ngozika N Okaisabor (Imo).

Sai Kudu maso Kudu akwai Ntong Festus Ntong (Akwa Ibom) da Nehizena Idemudia Afolabi (Edo) da Eberechi Suzette Wike (Ribas).

Yayin da Kudu maso Yamma akwai Lateef Babajide Lawal-Akapo (Legas) da Abiodun Azeem Akinyemi (Ogun) da Oyewumi Oyejoju Oyebiola (Oyo) da Bayo Ademola Taiwo (Oyo).

Wike ya raba abincin azumi ga Musulmai

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi rabon kayan abinci ga al'ummar Musulmai a birnin Tarayya.

Wike wanda ya kasance Kirista ya dauki wannan matakin ne ganin yadda jama'a ke cikin wani hali a fadin kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.