Tashin Hankali: Ana Fargabar Wasu sun Rasu Bayan Gini ya Rufto Musu a Kano
- Mutane da dama ne yanzu ke ke karkashin wani gini da ya fado musu a Kano, ana fargabar wasu sun ransu a iftila'in
- Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara a Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da faduwar ginin
- Ginin da ya fadi a Kuntau da ke karamar hukumar Gwale ya rufto kan al'umar da ke hada-hadarsu dazun nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano-Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce har yanzu ma'aikata na aikin zakulo wadanda gini ya rufta musu a Kano.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatarwa Legit Hausa cewa yanzu haka ana ta aikin ceton rai, kuma babu tabbacin adadin wadanda su ka rasu.
Ya kara da cewa jami'ansu da sauran jami'ai na ci gaba da kokarin zakulo wadanda ginin ya ruftawa domin ceton rai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani gini ne ya rufto kan mutanen da ke Kuntau, kuma zuwa yanzu ya ce ba a tantance adadin wadanda iftila'in ya shafa ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
An ceto mutum biyu daga baraguzai
An ceto akalla mutane biyu daga baraguzan ginin da ya fado a Kuntau da ke karamar hukumar Gwale.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa ana fargabar mutane 11 ginin ya danne.
Rahoton ya ce jami'an hukumar kare afkuwar hadurra ta FRSC ta garzaya da mutane biyun da aka ceto zuwa asibiti.
Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma ba a samu karin bayani kan halin da ake ciki ba.
Gini ya ruguzo kan wani jariri
Mun kawo mu ku labarin yadda wasu mazauna jihar Ondo sun shiga tashin hankali bayan gini ya fado kan wata uwa da jaririnta.
Dan uwan jaririn da kakarsa sun tsallake rijiya da baya, yayin da ake ta alhinin rashin mutum biyun.
Mutane da dama sun ji faduwar ginin, amma ba su iya kai agajin gaggawa wajen ceto mutanen ba, kamar yadda shaidun gani da ido su ka bayyana.
Asali: Legit.ng