Rai bakon duniya: Yadda wani gidan sama ya fado akan yaro dan shekara 3

Rai bakon duniya: Yadda wani gidan sama ya fado akan yaro dan shekara 3

Wani ibtila’i mai tsananin muni ya sake faruwa a jahar Legas, inda wani gidan sama mai hawa uku ya ruguje a unguwar Oju-ina dake yankin Agarawu na tsibirin jahar Legas, har yayi sanadiyyar mutuwar wani karamin yaro dan shekara 3.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Talata, 28 ga watan Mayu yayin da yaron tare dan biyunsa da mahaifiyarsu suke kwance a lokacin da wani gida dake makwabtaka dasu wanda ake shirin rusheshi saboda rashin cika ka’idojin gini ya afka kan gidansu.

KU KARANTA: Karshen alewa kasa: Aradu ta dira akan wani shahararren boka, ta halakashi

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da gidan ya fada akan gidansu marigayin, mahafiyarsa tayi kokarin ceto dan uwansa, amma ta manta dashi marigayi Kehinde Okedairo akan gado saboda tsananin rudewa.

Ba tare da bata lokaci ba jama’a suka taru suka fara dauke baraguzan ginin da nufin nemo yaron, amma hakan bai zo da sauki ba, har sai da aka dade ana kwashe baraguzan sa’annan aka hangi gawarsa kwance cikin jini.

Shugaban kungiyar mazauna yankin, Fatai Oriade ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace gwamnati ta dade da ayyana gidan a matsayin wanda zata rushe, inda ma ta sanya masa shaidar rushewa, amma bata aiwatar da hakan ba.

“A lokacin da muka ga gwamnati ta ayyana gidan a matsayin wanda zata rushe, sai muka bukaci dukkanin mazauna gidan dasu tashi don gudun aukuwar wani bala’in, muka kuma sanya ma gidan makulli. Gashi yanzu sakacin gwamnati yasa mun yi asarar karamin yaro.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: