Kudin Makarantar Ƴaƴan Yahaya Bello: Makarantar Amurka Za Ta Turawa EFCC $760,910
- Makarantar da Ali Bello, yaron tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya biya wa 'yan gidansu $845,852 sun tuntubi hukumar EFCC
- Makarantar Amurka da ke Abuja (AISA) ta sanar da EFCC cewa za ta mayar da $760,910 ga hukumar daga kudin da Bello ya biya
- EFCC na tuhumar tsohon gwamnan da karkatar da N80.2bn da kuma zargin ya yi amfani da kudin jihar wajen biyan kudin makarantar yaransa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Makarantar kasa-da-kasa ta Amurka da ke Abuja (AISA) ta ce za ta mayar da kudin makarantar da Yahaya Bello ya biya wa yaransa.
A cewar makarantar AISA, Yahaya Bello, wanda tsohon gwamnan jihar Kogi ne ya tura masu $845,852 na kudin makarantar yaransa har su kammala karatu.
A wasikar da mahukuntan makarantar suka aikawa hukumar EFCC, sun nemi a basu bayanan asusun banki domin mayar da kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta yi yunkurin kama Yahaya Bello
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa yanzu yaran Yahaya Bello na a matakin aji 2 zuwa 8 a makarantar ta AISA.
A ranar 17 ga watan Afrilu, jami'an hukumar EFCC suka dura gidan Yahaya Bello da ke Abuja a wani yunkuri na cafke shi kan badaƙalar N80.2bn.
A yayin da jami'an ke wannan kokari, Usman Ododo, gwamnan Kogi na yanzu ya ziyarci Yahaya Bello, inda aka yi zargin ya arce da shi.
"Za mu maido $760,910" Inji AISA
A cikin wasikar da ta aika wa EFCC shiyyar Legas, makarantar AISA ta ce $845,852 ne aka tura mata na kudin makarantar yaran a ranar 7 ga watan Satumba, 2021.
Sai dai AISA ta shaidawa EFCC cewa $760,910 kadai za ta iya mayarwa saboda ta cire kudaden sabis na makaranta kamar yadda yake a tsarinta.
A ranar 13 ga watan Agusta 2021 ne yaron Yahaya Bello, Ali Bello ya tuntubi makarantar kan yana so ya biya kudin makarantar 'yan gidan har su kammala.
Ali Bello ya yi karar makarantar AISA
Amma Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa Ali Bello ya maka makarantar AISA gaban kotu kan abin da ya kira "keta dokar yarjejeniya".
Ali Bello ya shigar da karar ne saboda makarantar ta fara tattaunawa da hukumar EFCC kan duba yiwuwar turawa gwamnati kudin da Bello ya turawa makarantar.
Tun a 2023 hukumar EFCC ke bibiyar makarantar AISA kan batun kudin makarantar da iyalan Yahaya Bello suka biya, tare da zargin kudin baitul mali ne ya yi amfani da su.
Yadda EFCC ta yi da Yahaya Bello
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ki amsa gayyatar su.
Olukoyede ya ce duk wani kokari da EFCC take yi na mutunta tsohon gwamnan ya tashi a banza inda Yahaya Bello ya ci gaba da yin wasan 'yar buya da jami'ansu.
Asali: Legit.ng