Zaben Ciyamomi: Gwamnan APC Ya Rushe Shugabannin Kananan Hukumomi 17

Zaben Ciyamomi: Gwamnan APC Ya Rushe Shugabannin Kananan Hukumomi 17

  • Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da cewa ta rusa dukkanin shugabannin riko na kananan hukumomi 17 da da kansilolinsu
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ta jihar Yobe (YSIEC) ta sanya ranar 25 ga watan Mayu domin gudanar da zaben ciyamomi
  • Sakataren yada labarai na gwamnatin jihar Yobe, Malam Shuaibu Abdullahi ya ce wa'adin shugabannin rikon na watanni shida ya kare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da rusa dukkanin shugabannin kananan hukumomi 17 da da kansilolinsu.

Gwamnatin Yobe ta sauke shugabannin kananan hukumomi
Gwamna Ma Mala Buni ya ba da umarnin sauke ciyamomin riko 17 na jihar Yobe. Hoto: @MalaBuni
Asali: Twitter

Sakataren yada labarai na gwamnatin jihar, Malam Shuaibu Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

YSIEC za ta yi zaben kananan hukumomi

Ya ce Gwamna Buni ya umarci dukkan ciyamomin da su mika ragamar ayyuka ga daraktocin gudanarwa na kananan hukumomin a yau ranar 25 ga Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Yobe (YSIEC) ta sanya ranar 25 ga watan Mayu domin gudanar da zaben ciyamomi.

An tattaro cewa wa’adin watanni shida na shugabannin kananan hukumomin da aka debar masu ne ya kare yanzu.

Ma'aikatan Yobe ba sa bin gwamnati bashi

A baya Legit ta ruwaito yadda Gwamna Mai Mala Buni ya bugi kirji da cewa jiharsa ta Yobe na daga cikin jihohin da ma'aikata ke samun albashi a kan kari.

A yayin da yake kara jaddada cewa ma'aikata ba sa bin gwamnati bashin albashi a jihar, Gwamna Buni ya nemi ma'aikata su rike amana da yin aiki tukuru.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: An gargadi Tinubu ya dauki mataki kan EFCC game da tsohon gwamna

Wannan na zuwa ne yayin da wata kafar fasaha ta BudgIT ta fitar da rahoto kan jihohin da ba sa iya biyan ma'aikatansu albashi a Najeriya.

Rashin bankuna a jihar Yobe

A wani labarin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya koka kan yadda kananan hukumomi hudu ne kacal ke da banki a fadin jihar.

Mai taimakawa Gwamna Buni a kan harkokin sadarwa Mamman Mohammed, ya bayyana hakan yana mai cewa al'umar jihar na shan wahala wajen hada-hadar kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.