Saura Kwana 9 wa'adin tsaffin Naira: Kananan Hukumomi 4 Kacal Ke da Banki a Jihar Yobe, Mai Mala ya koka

Saura Kwana 9 wa'adin tsaffin Naira: Kananan Hukumomi 4 Kacal Ke da Banki a Jihar Yobe, Mai Mala ya koka

  • Al'ummar Yobe na cikin damuwa mai tsanani kan batun sauyin sabbin kudi da babban bankin kasa ya fito dashi
  • Gwamnan jihar Mai Mala Buni ya roki bankin kasa CBN, da ya duba yiwuwar tsawaita kwanakin sauyin kudi
  • Jihar Yobe nada karancin bankunan da za'a yi mu'amala da su wajen sauya ko samun sabbin kudade

Yobe - Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya roki da babban bankin kasa (CBN) da su kara wa'adin karbar kudin zuwa wani lokaci kan wanda suka yanke.

Mai yasa gwamna yayi wannan sanarwar?

Sanarwar wadda gwamnan yai wannan rokon na cikin wata takarda ne da mai taimakawa gwamna harkokin sadarwa Mamman Mohemmed, a ranar Lahadi, ya fitar.

Gwamnan yace ya kamata babban bankin kasa CBN, ya kara wa'adin zuwa wani lokaci.

Kara karanta wannan

Haren-haren da ake kaiwa cikin daji mata da yaran Fulani kawai ake kashewa, Gumi

Mai Mala
Yayin Da Wa'adin Da Babban Bankin Kasa Ke Cika, Kananan Hukumomi Hudu Ne KAwai Suke Da Banki A Yobe Hoto: UCG
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar tayi bayani cewa a kananan hukumomin sha 17 da ke Jihar Yobe, guda hudu ne kawai suke da bankunan kasuwanci a jihar, wanda hakan zai wahala da yan Yoben su samu damar canja kudin zuwa wa'adin da aka deba ya cika.

A cewarsa:

"Wasu daga cikin bankunan, basu da rassa a kananan hukumomi, wasu kuma bankunan sun kasance a rufe, sabida matsalar rikici da tashin-tashinan kungiyar Boko Haram
"Ya kamata babban bankin kasa CBN, ya duba wannan yanayin da muke ciki, sabida a magance wannan matsalar a tsakanin jam'ar jihar Yobe"
"A matsayinku na masu sarrafa harkokin kudi na kasar nan, ya kamata a bude bankunan kasuwanci da su fitar da wata hanya za'a sauaka wajen sauyin kudin"

Buni ya ci gaba da cewa akwai bukatar a tsaurara tsaro wajen kula da harkokin tsaro dan inganta yadda za'a gudanar da aiyukan canjin kudin a yankin, kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: CBN ya kawo mafita ga mutanen kauye, ya kawo wani sabon tsari mai kyau

Akwai Bukatar gaggawa

Akwai bukatar a dau mataki na gaggawa, amma in ba haka ba, akwai yiwuwar da yawa daga cikin mutane mu zasu rasa kudadensu.

"A matsayina na lamaba daya a jihar nan naga akwai wannan matsalar kuma akwai bukatar ace a maganceta sabida irin abubuwan da muke hange kuma muke gani"

Har yanzu dai babban bankin kasa ya tubure kan dole sai kowa ya sauya kudinsa kafin wa'adin da ya dauka ya cika.

Wasu Sun daina karban tsoffin kudi

Wasu shaguna da suke unguwar sharada a jihar kano sun dai karbar tsoffin kudi, gabannin wa'adin da babban bankin kasa ya cika.

Masu kantunan sun shedawa wakilin Legit.ng Hausa cewa sun dau matakin ne dan gujewa asara in sun karbi tsoffin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel