Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe

Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe

- Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe

- Hakazalika yan takarar kansiloli na jam’iyyar 178 duk sun kawo unguwanninsu

- An tattaro cewa APC ce kadai ta tsayar da yan takara a zaben ciyamomin

Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Yobe ta share dukkan zabukan shugabannin kananan hukumomi 17 da aka yi a jihar.

'Yan takara 178 na zaben kansiloli, suma sun lashe dukkan unguwanni a cikin gundumomin sanatoci uku.

KU KARANTA KUMA: Rana bata karya: Ganduje ya saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano

Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe
Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe Hoto: Bioreport
Asali: UGC

Da yake sanar da sakamakon zaben kansiloli a karshen mako a Damaturu, babban birnin jihar, babban sakatare na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe (YBSIEC), Dokta Mamman Mohammed ya bayyana cewa:

“Daga cikin jam’iyyun siyasa shida da suka fafata a zaben, APC ce kadai ta fitar da‘ yan takarar ta; yayin da wasu jam’iyyu biyar suka tsaya takarar zaben kansiloli kawai.”

Ya lura cewa a zabukan ciyamomi, babu wani dan adawa ko ‘yan takara daga wasu jam’iyyun siyasa da suka shiga zaben, jaridar Vanguard ta ruwaito.

"APC ce kawai ta fitar da 'yan takarar zaben ciyamomi da kansiloli," ya kara da cewa masu zaben sun zabi jam'iyyar.

Ya ce fitar da ‘yan takarar jam’iyyar ya yi daidai da dokokin zabe.

A cewarsa, kalubalen da hukumar kawai ta samu shi ne sauran jam’iyyun adawa biyar su cike gurabensu na ciyamomi.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a Neja cikin sa’o’i biyu, sun kashe 3 da yin garkuwa da wasu da dama

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yabawa Salihu Tanko Yakasai, hadimin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da aka sallama saboda sukar Buhari a shafinsa na Twitter.

Fayose ya yi wannan jinjinan ne bayan Alhaji Tanko Yakasai, mahaifin Salihu Tanko Yakasai ya bada rahoton cewa jami'an tsaro sun kama dansa saboda ya ce Shugaba Buhari ya yi murabus yayin Allah wadai da sace ɗaliban GGSS Jangebe a jihar Zamfara.

Amma, Fayose ya ce matakin da Yakasai ya ɗauka ya maida shi jarumin demokradiyya kuma alama ce da ke nuna haɗin kan Nigeria.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel