Yahaya Bello: EFCC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Janye Korafin da Ta Shigar Kan Tsohon Gwamnan
- Yayin da ake ci gaba da tuhumar Yahaya Bello, hukumar EFCC ta yi amai ta lashe kan daukaka kara da ta yi
- Hukumar ta janye korafin da ta shigar da ke kalubalantar neman kama tsohon gwamnan da ta ke yi a Najeriya
- Wannan ya biyo bayan hukuncin kotun inda ta dakatar da hukumar daga kama Yahaya Bello kan badakalar N84bn
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta janye korafi da ta shigar kan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Hukumar ta sanar da janye daukaka kara da ta shigar kan dakatar da ita da kotu ta yi kan kama tsohon gwamnan.
Musabbabin korafin da EFCC ta shigar
EFCC ta shigar da korafi ne inda ta ke kalubalantar kotun kan matakin da ta dauka game da kama Yahaya Bello kan badakalar N84bn, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata takarda dauke da korafin a ranar 22 ga watan Afrilu, EFCC ta ce ta janye ne saboda wasu abubuwa da dama sun sha karfin korafin da ta shigar.
Ta kuma tabbatar da cewa ta shigar da korafin ne a kotu kan Yahaya Bello bayan lokaci ya kure kamar yadda doka ta tanadar, cewar Vanguard.
Sanarwar yanye korafi daga EFCC
"Mai shigar da kara ta na sanar da janye korafinta kan wanda ake zargi kan maudu'in da ake magana a kai."
"Sanarwar janye karar ta tabbatar da cewa a ranar 17 ga watan Afrilu, matakin da babbar kotun jihar Kogi ta dauka ya jibanci korafin nata."
- EFCC
Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke neman tsohon gwamnan ruwa a jallo kan badakalar N84bn lokacin da ya ke mulkin jihar Kogi.
An ba Tinubu shawara kan Yahaya Bello
A wani labarin mai kaman da wannan, Gamayyar jam'iyyun siyasa ta UPPP reshen jihar Kogi ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan dambarwar Yahaya Bello.
Kungiyar ta bukaci Tinubu ya ja kunnen hukumar EFCC game da yadda ta ke gudanar da bincikenta kan tsohon gwamnan Kogi.
Yayin tattaunawa da manema labarai, Ibrahim Itodo ya ce ya kamata hukumar ta yi hankali kan binciken tare da bin dokar kasa.
Asali: Legit.ng