Majalisar Dokokin Kaduna Ta Fara Binciken Nasir El Rufa’i Watanni 10 da Barin Mulki

Majalisar Dokokin Kaduna Ta Fara Binciken Nasir El Rufa’i Watanni 10 da Barin Mulki

  • Majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara binciken tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, a kan mulkinsa daga 2015 zuwa 2023
  • Majalisar ta lissafa abubuwan da suka shafi harkokin kudi da binciken zai shafa tare da kafa kwamitin wucin gadi da zai yi aikin
  • Ana sa ran kammala binciken ne cikin gaggawa kamar yadda Majlisar ta ba kwamitin wa'adin da zai kawo mata muhimman takardu da ta ke buƙata.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara binciken a kan yadda tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya gudanar da harkokin kudi a lokacin gwamnatinsa.

malam Nasiru
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara binkicen gwamnatin El-Rufa'i. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

An ruwaito cewa binciken zai shafi shekaru takwas da Malam Nasir El-Rufai ya yi yana mulki, daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Majalisa ta tura bukata ma'aikatar kudi kan binciken badakala

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa majalisar ta yi wa kwamishinar kudi ta jihar, Sakinatu Hassan Idris bayani a kan yadda binciken zai gudana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta kafa kwamitin binciken El-Rufai

Majalisar ta bayyana a zamanta na 150 a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu cewa ta kafa kwamitin wucin gadi domin gudanar da binciken tsohon gwamnan.

Kwamitin binciken an kafa shi ne bisa yadda dokokin majalisar da dokokin tarayyar Najeriya suka suka tanadar, cewar jaridar Punch

Abubuwan da ake binciken El-Rufai a kai

A cewar majalisar, binciken zai shafi harkokin kudi gaba daya wadanda suka hada ba karban bashi da bada lamuni daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Daga cikin abubuwan da binciken zai shafa akwai maganar biyan albashi daga shekarar 2016 zuwa 2022.

Har ila yau akwai btun bada lamuni wadanda suka hada da dalilin bada lamunin da sharudansa.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

Haka zalika za a duba kuɗaɗen da aka biya 'yan kwangila da bayanan 'yan kwangilar da gwamnatin tayi aiki da su daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Magatakardan majalisar dokokin ya tabbatar da cewa binciken ana bukatar kammala shi cikin gaggawa.

Rahotanni sun kara da cewa ana so kwamitin wucin gadin ya kammala tattaro muhimman takardun binciken ga majalisar zuwa ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu da karfe 10.00 na safe.

Dalilin binciken gwamnatin El-rufa'i a Kaduna

A wani rahoton kuma, kun ji cewa kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya yi magana kan dalilin da ya sa aka kafa kwamitin binciken Nasir El-Rufai

Liman ya bayyana cewa za a gudanar da binciken ne domin nuna cewa majalisar da yake jagoranta ba ta amshin shatar bangaren zartarwar ba ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng