Yahaya Bello ya Dauki $720,000 ya Biya Kudin Makarantar Yaronshi a Waje, Shugaban EFCC

Yahaya Bello ya Dauki $720,000 ya Biya Kudin Makarantar Yaronshi a Waje, Shugaban EFCC

  • Hukumar EFCC ta ce bincikenta ya gano yadda tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello ya kwashi daloli daga asusun jihar tare da kai su kasuwar canji
  • Shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja inda ya ce Yahaya ya kwashe dala dubu 720 daga baitul mali
  • Ola Olukoyede ya yi barazanar ajiye aiki muddin aka samu katsalandan na dakatar da binciken Yahaya Bello domin, ya ce sai ya ga karshen shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Shugaban hukumar hana yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC), Ola Olukoyede ya zargi tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello da cirar kudi daga asusun gwamnati don biyawa yaransa kudin makaranta.

Kara karanta wannan

Badakalar $720, 000: Yadda muka yi da tsohon gwamna Yahaya Bello Inji Shugaban EFCC

Ola Olukoyede ya ce Yahaya Bello ya ciri dala dubu 720, inda kai tsaye ya nufi kasuwar canji aka musanya masa, sannan ya biyawa yayansa kudin makaranta na gaba.

EFCC ta ce ba za ta daga kafa wajen bincikar Yahaya Bello ba
Ana zargin Yahaya Bello da yin canjin dala dubu 720 don amfanin kashin kai Hoto:Alhaji Yahaya Bello/Ola Olukoyede
Asali: Facebook

Yahaya Bello da hukumar EFCC?

Shugaban ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a Talatar nan a babban birnin Tarayya Abuja, kamar yadda wani mai sharhi @UGo, @Oforma19 ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa Yahaya Bello ya wawushe kudin baitul malin ne daf da zai bar kujerar gwamnan jihar.

Shugaban ya ce akwai takardun shaidar cirar kuɗin da na sauran tuhume-tuhumen da ake yi wa Yahaya Bello, kuma hukumar za ta bawa duk wanda ya bukata.

Shugaban EFCC ya yi barazanar ajiye aiki

Mista Ola Olukoyede, shugaban hukumar EFCC ya yi barazanar ajiye aiki matukar ba a binciki tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ba.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Shugaban EFCC na ƙasa ya sha alwashin yin murabus daga muƙaminsa

Ya ce zai bi bincike da gurfanar da Yahaya gaban kotu, domin sai ya ga karshen shari'ar, Channels Television ta wallafa labarin nan.

Shugaban ya kuma ce za a hukunta dukkanin wadanda su ka taka rawa wajen jinkirta kama Yahaya Bello domin ya fuskanci tuhumar da ake yi masa.

Kotu ta amince a cafko Yahaya Bello

Mun kawo mu ku cewa mai Shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kogi ya bawa EFCC damar cafke tsohon gwamnan jihar duk inda aka gan shi.

EFCC na zargin tsohon gwamna Yahaya Bello da tatike lalitar gwamnatin jihar, inda ya wawure naira miliyan 84 daga asusun.

Tuni EFCC ta fara binciken Yahaya Bello, inda ta samu hadin kan rundunar yan sanda da hukumar shige da fice ta kasa domin ayi tara-tara a kamo shi ya fuskanci shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.