"Zan Biya N200,000": Bobrisky Ya Saukar da Kai, Ya Nemi Alfarma Kan Hukuncin Kotu

"Zan Biya N200,000": Bobrisky Ya Saukar da Kai, Ya Nemi Alfarma Kan Hukuncin Kotu

  • Yayin da aka daure shi har na tsawon watanni shida, ɗan daudu Idris Okuneye ya nemi alfarma kan hukuncin kotun
  • Bobrisky ya bukaci kotun ta yi masa sassauci wurin sauya zaman gidan kaso zuwa kudi N200,000 domin ya biya
  • Wannan na zuwa ne bayan alkalin kotun a jihar Legas, Abimbola Awogboro ya yanke masa hukunci kan cin mutuncin naira

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye ya roki alfarma kan hukuncin da aka yanke masa a Legas.

Ɗan daudun da aka fi sani da Bobrisky ya roki alfarmar a sauya masa zaman gidan yarin zuwa tsurar kudi domin ya biya.

Kara karanta wannan

Ganduje: An sake bankado yadda tsohon gwamnan ya karkatar da N51.3bn, an gano dalili

Bobrisky ya roki alkalin kotun da ya yanke masa hukunci
Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya bukaci biyan N200,000 kan laifuffukansa. Hoto: @Bobrisky222.
Asali: Instagram

Wace alfarma Bobrisky ya nema a kotu?

Lauyan ɗan daudun, Bimbo Kusanu shi ya yi wannan roko inda ya bukaci mayar da laifuffukan kowane guda daya N50,000, a cewar BusinessDay.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai kare dan daudun ya bukaci hakan ne domin Bobrisky ya biya N200,000 kan dukkan korafe-korafen da ke yi kansa domin samun sauƙi.

Wannan ya biyo bayan daure Bobrisky da alkalin kotun, Abimbola Awogboro ya yi na tsawon watanni shida ba tare da biyan tara ba.

An yanke masa wannan hukunci ne kan zargin cin zarafin Naira da kuma wulakanta ta da ya yi wanda ya amsa laifinsa, cewar rahoton ThisDay.

An bayyana inda za a ajiye Bobrisky

Har ila yau, Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya (NCS) ta bayyana sashen da za ta ajiye dan daudu, Idris Bobrisky.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya dara su", Jigon APC ya fadi yadda Najeriya za ta kasance a hannun Atiku da Obi

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan fitaccen ɗan daudun ya bayyanawa kotu cewa shi namiji ne.

Hakan ya biyo bayan bayyana jinsinsa da Bobrisky ya yi a gaban alkalin kotun da ke jihar Legas yayin da ake gudanar da shari'ar.

Kotu ta yankewa Bobrisky hukunci

A wani labarin, kun ji cewa Babbar kotun Tarayya da ke jihar Legas ta saka ranar yanke hukunci kan ɗan daudu, Idris Okuneye.

Kotun ta tanadi hukunci kan ɗan daudu, Bobrisky domin yanke masa hukuncin a ranar 9 ga watan Afrilun wannan shekara da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.