Murna Yayin da Gwamnan APC Ya Rage Kuɗin Karatu a Jami'a, Ya Karawa Ma'aikata Albashi
- Gwamna Francis Nwifuru ya rage kashi 10% na kudin makarantar da ɗalibai ke biya duk shekara a jami'ar jihar Ebonyi
- Bayan haka kuma gwamnan ya ƙara wa malamai da ma'aikatan jami'ar albashi da kashi 20% da 10% domin ƙara masu kwarin guiwa
- Nwifuru ya faɗi haka ne a wurin taron yaye ɗaliban jami'ar ranar Asabar da ta gabata, inda ya ja hankalin ɗaliban su zama masu amfanar kasar su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya rage kudin karatun jami'ar jihar da kashi 10 cikin 100 domin rage tsadar kudin makarantar.
Gwamnan ya kuma amince da ƙarin albashi na kaso 20% ga malamai da kaso 10% ga ma'aikatan jami'ar jihar Ebonyi, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Nwifuru ya sanar da haka ne a wurin taron yaye talibai karo na 12 zuwa 15 da aka haɗa lokaci guda ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun gwamnan, Monday Uzor, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Gwamna Nwifuru ya ɗauki alƙawari
Mista Nwifuru ya kuma bayyana cewa ’yan asalin jihar da suka kammala karatun digiri da daraja ta farko (First Class) za a ɗauke su aiki a matsayin mataimakan malamai.
Sai dai babu tabbas ko gwamnatin Ebonyi tana da wani shiri da bada irin wannan dama ga ɗalibai ’yan asalin jihar da suka kammala karatun digiri da matakin daraja ta farko a wasu makarantun.
Bugu da ƙari, Gwamnan na jam'iyyar APC ya ce ya ƙara yawan kuɗin kasafin jami'ar daga N200m zuwa N280m duk wata domin ƙara inganta harkar ilimi.
Nwifuru ya ja hankalin ɗaliban
A jawabinsa na wurin taron, Gwamna Nwifuru ya ce yaye ɗaliban wata dama ce gare su ta ba da gudummuwa a ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan ya kuma ja hankalin ɗaliban da aka yaye da su yi amfani da maslaha ta gida wajen warware matsalolin yankinsu maimakon su fito suna neman agaji daga waje.
Ya bukace su da su yi amfani da ilimin da suka samu a jami’ar wajen magance matsalolin da ke addabar kasar nan, cewar rahoton AIT.
Shekarun shiga jami'a a Najeriya
A wani rahoton kuma Gwamnatin Bola Tinubu ta fara shirin aiwatar da shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun shiga jami'a a Najeriya.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce a yanzu za ka ga ɗalibai ƴan shekara 15 da 16 suna zana jarabawar JAMB.
Asali: Legit.ng