"Daliban da Suka Fi Kowa Kokari a Jarrabawar JAMB Daga 2014 Zuwa 2023"
- Kamfanin tattara alkaluma ta StatiSense ta fitar da jerengiyar dalibai da suka fi kowa kokari a jarrabawar JAMB cikin shekaru 10 da suka wuce.
- Kididdigar da ta fara daga shekarar 2014 zuwa 2023 ta fitar da daliba mace ce a matsayin wacce ta fi kowa kokari yayin da na miji ke bi mata baya
- Har ila yau, kididdigar ta nuna dalibai sama da 32 da suka samu maki daga 350 zuwa sama cikin dalibai sama da 60
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kamfanin tattara alkaluma na StatiSense ya fitar da jerengiyar dalibai da suka yi zarra a jarrabawar JAMB cikin shekaru 10 da suka wuce.
Zakarun Jarrabawar JAMB a Najeriya
Jerengiyar da kamfanin ya fitar ya fara ne daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2023 kuma ta fitar da adadin talibai sama da 60 da suka yi zarra a cikin shekarun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kididdigar da aka fitar a shafin X, ya nuna Maduafokwa Agnes a matsayin wacce ta fi kowa samun maki a cikin shekarun, ta samu maki 365. Sai kuma dalibi na miji mai bi mata baya, Galadima Zakari, da ya samu maki 364
Agnes dai ta rubuta jarrabawar ne a shekarar 2020 yayin da Zakari kuma ya rubuta ta a shekarar 2018.
A cikin kididdigar, dalibai mafi rinjaye maza ne, duk da cewa wacce ta fi kowa samun maki mace ce. A cikin daliban sama da 60 da suka yi zarra, guda 13 ne kawai mata sauran duk maza ne.
Ɗalibai guda 32 ne suka samu maki daga 250 ya yi sama yayin da sauran suka samu kasa da haka.
JAMB: Jerengiyar gwarazan dalibai maza
1. Galadima Zakari - 364 (2018)
2. Nwobi David - 363 (2020)
3. Adebayo Oluwatofunmi - 362 (2022)
4. Anonye Emenike - 359 (2016)
5. Elikwu Chukwuemeka - 359 (2020)
6. Ugwu Innocent - 359 (2022)
7. Adekunle Jesufemi - 358 (2018)
8. Adebola Paul - 358 (2020)
9. Monwuba Chibuikem - 358 (2021)
10. Aguele Stephen - 358 (2023)
11. Ositade Oluwafemi - 358 (2023)
12. Alikah Oseghale - 357 (2018)
13. Emmanuel Temiloluwa - 357 (2022)
14. Ozumba Ikemsinachukwu - 357 (2022)
15. Gbolahan Ayinde - 357 (2023)
16. John Fulfilment - 356 (2023)
17. Ademola Adetola - 355 (2018)
18. Chimdubem Ugonna - 355 (2023)
19. Obi-Obuoha Abiamamela - 354 (2018)
20. Ape Moses - 354 (2018)
21. Akinyemi Paul - 354 (2018)
22. Akingbulugbe Ayomide - 353 (2017)
23. Ifeanyi Akachukwu - 350 (2016)
24. Adeogun Oreoluwa - 350 (2021)
25. Qomarudeen Alabi - 350 (2021)
26. Utuk Joseph - 349 (2017)
27. Ajayi Isaiah - 349 (2021)
28. Fatoke Paul - 346 (2017)
29. Oladiran Oluwabukunmi - 346 (2017)
30. Fasoro Sunday - 346 (2017)
31. Ezeobiukwu Odinaka - 346 (2017)
32. Igban Chidiebube - 346 (2019)
33. Olowu Olamilekan - 345 (2019)
34. Odo Obinna - 344 (2019)
35. Okezie Emmanuel - 343 (2019)
36. Orisakwe Chiebuka - 343 (2019)
37. Peters Gbenupo - 312 (2015)
38. Adewole Richard - 306 (2015)
39. Ugwuanyi Chidera - 306 (2015)
40. Olise Chukwunalu - 299 (2013)
41. Onomejoh Princewill - 299 (2014)
42. Eruobodo Adedamola - 297 (2013)
43. Soladoye Faith - 297 (2014)
44. Bala Yusuf - 296 (2013)
45. Uwaoma Chigozie - 296 (2013)
46. Arienmughare Oghenetega - 296 (2013)
47. Adeboye Emmanuel - 291 (2014)
48. Deshi Micah - 290 (2014)
49. Ogunduyilemi Adedayo - 290 (2014)
JAMB: Jerengiyar gwarazan dalibai mata
1. Maduafokwa Agnes - 365 (2020)
2. Umeh Nkechinyere - 360 (2023)
3. Akenbor Osarugue - 359 (2016)
4. Ojuba Shalom - 359 (2020)
5. Ugwuoke Chinelo - 358 (2016)
6. Igbalaye Kathryn - 357 (2022)
7. Adedini Diana - 351 (2016)
8. Okarike Favour - 348 (2021)
9. Okoroafor Lucy - 347 (2017)
10. Ilukwe Geraldine - 332 (2015)
11. Okorie Modestar - 325 (2015)
12. Obrimah Oluwawunmi - 290 (2014)
JAMB ta dauki mataki kan jami'anta
A wani rahoton kuma, kun ji cewa yayin da wasu jami’an hukumar JAMB suka bukaci wata daliba sanye da hijabi da ta cire yayin tantancewa, an dauki mataki a kansu.
Hukumar ta tabbatar da cewa ta dauki matakin ne domin ya zama izina ga sauran jami’anta da ke shirin aikata haka a nan gaba.
Asali: Legit.ng