Malaman Musulunci Sun Shiga Gargadin DisCos a Kan Lalacewar Wutar Lantarki
- Malaman musulunci sun yi tir da karancin wutar da ake fuskanta a lokacin da ake fama da matsanancin zafi a kasar nan
- Sheikh Salihu Shu’aibu ya ce a haka aka yi azumi, sannan har gobe ba a samun wuta a irinsu Tudun Wada da ke Zariya
- A wajen wani wa’azi, Alkali Abubakar Salihu Zaria ya ja-kunnen ma’aikatan lantarki game da halin da ake ciki a yau
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Matsalar wutar lantarki ta ta’azzara sosai a wasu wurare musamman a ‘yan kwanakin baya-bayan nan a Najeriya.
Wannan yanayi ya jawo har malaman addini suka fara fitowa suna tir da ma’aikatan DisCos masu aikin raba wutar lantarki.
Ba a samun lantarki a Tudun Wada
A wani bidiyo da kafar Al-Haqq ta wallafa a shafinta na Facebook, an ji Sheikh Salihu Shu’aibu Zariya yana kokawa da rashin wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Salihu Shu’aibu Zariya ya yi kira ga kamfanonin na DisCos da gwamnatocin jiha da tarayya cewa ba a samun wuta a Zariya.
Malamin ya yi magana a game da yankinsa na Tudun Wada da ke karamar hukumar Zariya, ya ce batun wutar lantarki ya tabarbare.
Shehin malamin ya yi maganar tsarin da DisCos suka kawo na kasa unguwanni daidai da adadin awannin wuta da za su rika samu.
Zaluncin kamfanonin wutar lantarki
Malamin musuluncin ya ce akwai nau’in rashin adalci ganin wutar awanni hudu za a rika ba Tudun Wada da sunan ba a biya kudi.
A daidai wannan lokaci kuma Legit ta fahimci ana samun wuta sosai a unguwannin GRA, PZ da makarantun Aviation da ABU Zariya.
A cewarsa, zaluncin sun hada da rashin raba isasshiyar wuta, kin gyara turansfoma da cigaba da karbar kudi ko turansfoma ta tsaya.
Rashin wutan lantarki ya hana Alkali barci
Shi ma Shiekh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi wannan Allah-wadai a wani wa’azi kamar yadda muka ci karo da bidiyonsa a X.
Alkalin ya koka kan yadda ake fama da karancin wutar lantarki musamman a lokacin nan da ake fama da tsananin zafi.
Wannan malami da ya shahara ya ce haka zafi ya hana shi barci a gida kwanakin baya.
Matsalar rashin wutar lantarki a rayuwa
Salihu Shu’aibu Zariya ya ce rashin wuta yana kawo matsala ga kiwon lafiya, ibada da karatu har zuwa abincin da jama'a za su ci.
Darektan na cibiyar Al-Islah ya ce idan abubuwa suka gaza sauya zani, ma’aikatan da ke karbar kudin lantarki suna cikin barazana.
A karshe ya yi kira ga talakawa da sauran jama’a su rika biyan kudi muddin an ba su wuta tare da jawo hankalin shugabannin jihar.
Halin da talakawan Najeriya suke ciki
Kwanakin baya an kawo maku labari cewa Shuaibu Salihu Zariya ya ankarar da masu mulki a halin da al’umma su ka shiga.
Malamin ya roki gwamnati ta fito da tsare-tsaren rage radadin talauci da matsin lamba domin jama’a su ci moriyar damukaradiyya.
Asali: Legit.ng