NDLEA ta Gargadi Matafiya Kan Hanyar da Ake Iya Aukawa Cikin Matsla

NDLEA ta Gargadi Matafiya Kan Hanyar da Ake Iya Aukawa Cikin Matsla

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, (NDLEA) ta gargadi matafiya kan rike jakar da ba su san abin da ke ciki ba
  • Femi Babafemi, darakatan yada labaran hukumar ne yayi jan kunnen a yau Lahadi ta shafinsa na X inda ya ce ana iya fadawa matsala
  • Ya ce da kyar su ka taimaki wasu dalibai biyu daga hannun mahukunta bayan samun kodin a jakar da wata daliba ya ba su sallahu su kai mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gargadi matafiya da kada su kuskura su yi rikon jakar da ba su san abin da ke ciki ba.

Kara karanta wannan

Hukumar JAMB ta dauki mataki kan wasu jami'anta da suka ci zarafin daliba mai hijabi

NDLEA ta yi gargadin za a iya rikon jaka mai dauke da kwayoyi da sauran abubuwan maye da zai zama gagarumin laifi, musamman idan aka kama wanda ke dauke da jakar.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa
Hukumar ta NDLEA ta yi gargadin rikon jakunkunan da ba san kayan ciki ba ka iya zama matsala Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran hukumar, Femi Babafemi ne ya yi gargadin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yau Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana fargabar wadanda ba su ji ba su gani ka iya fuskantar hukunci idan aka kama su da jakunkunan masu dauke da kwayoyi da sauran kayan maye.

An kama dalibai da jakar kodin

Femi Babafemi ya bayyana cewa hukumomi a wata kasa sun cafke wasu yan Najeriya guda biyu bayan an gano kwalaben kodin a jakar da wata daliba ta basu riko.

Dalibar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta bawa wasu dalibai biyu ciki har da mai karatun digiri na 3 sallahun jakarta.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Sai bayan hukumomi na duba jakunkunan matafiya kamar yadda aka saba sai aka gano kwalaben kodin din, kamar yadda kafar Channels Television ta wallafa.

A kalamansa:

" Da tuni suna gidan yari ba dan @ndlea_nigeria ta yi kokari wajen dawo da aihinin mai jakar gida ba "
"Wannan shi yasa mu ke jan kunne kada wanda ya dauki jakar da bai san abin da ke ciki ba daga hannun kowa."

NDLEA ta kama masu ta'ammalli da kwayoyi

A baya kun samu labarin yadda hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wasu mutane 319 da ake zargi da ta'ammalli da miyagun kwayoyi a jihar Kano.

kwamandan hukumar reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya shaidawa manema labarai cewa akwai mata 14.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.