An kama wani mutum dauke da kwalaben kodin 300 a jihar Katsina

An kama wani mutum dauke da kwalaben kodin 300 a jihar Katsina

Yan makonni kadan bayan gwamnatin tarayya ta haramta kodin, an kama wani mai hada magunguna na bogi kuma dilan miyagun kwayoyi, Nura Aliyu, dauke da maganin kodin kwali shida da kuma kwalaye 142 wanda an rigada an saida su a jihar Katsina.

Yan sanda jihar Katsina sun gurfanar da Aliyu mai shekaru 30 a hedkwatarsu a jiya, tare da miyagun magunguna kwali shida wanda daidai yake da kwalabe 300 da kuma kwalaye 142 da babu komai ciki da kuma motar da yayi amfani da shi wajen safarar haramtattun kayayyakin.

A lokacin da ake gurfanar da mai laifin, kwamishinan yan sandan jihar, Mohammed Wakili yace an kama shi ne a hanyar Sanata Abba Ali Road ta hanyar Mohd Dikko Stadium.

An kama wani mutum dauke da kwalaben kodin 300 a jihar Katsina
An kama wani mutum dauke da kwalaben kodin 300 a jihar Katsina
Asali: Depositphotos

A nashi bangaren, Aliyu yace Allah ya shirya faruwan haka amma yayi danasanin abunda ya aikata.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sandan Minna, jihar Niger sun kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Shamsu Abubakar inda yake shiga irin ta mata yana damfarar maza.

KU KARANTA KUMA: Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC

An kama shi ne sanye cikin hijabi da zani, inda ya sha kwaliyya sannan yasa takalmi da jaka iri guda na mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel