An Shiga Jimami Bayan Wasu Almajirai 7 Sun Rasu a Wani Yanayi Mara Dadi a Jihar Kebbi

An Shiga Jimami Bayan Wasu Almajirai 7 Sun Rasu a Wani Yanayi Mara Dadi a Jihar Kebbi

  • Wasu almajirai sun rasa rayukansu bayan wani rami ya rufta da musu a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi ta jihar Kebbi
  • Ɗaliban dai sun je ɗebo ƙasa ne domin gyara ramukan da ke cikon ɗakunansu lokacin da ramin ya rufta da su
  • Shugaban makarantar da suke karatu ya nuna alhininsa kan lamarin inda ya ce shi ne ya sanya su zuwa ɗebo ƙasar domin su yi gyaran

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Wani rami ya rufta kan almajirai takwas na makarantar Kur’ani ta Malam Dan-Umma da ke Bayan Science, unguwar Badariya a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a Jihar Kebbi.

Lamarin ya auku ne a jiya Asabar, 20 ga watan Afirilun 2024 inda bakwai daga cikinsu suka rasu, sauran kuma suka jikkata.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mazauna kauyen Zamfara sun nemi mafaka a gidan gwamnati

Almajirai 7 sun rasu a Kebbi
Almajiran sun je debo kasa ne lokacin da lamarin ya auku Hoto: Nasir Idris
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa shugaban makarantar Malam Dan Umar ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a gidansa da ke harabar makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Ya ce ya sanya ɗaliban su je saman tudun da ke kusa da makarantar don ɗeɓo ƙasar da za su gyara ramukan da ke cikin daƙunansu, rahoton jaridar Leadership ys tabɓatar.

Umar wanda ya yi magana cikin hawaye, ya ce ana cikin haka ne sai ƙasar ta zaftaro ta faɗo musu, inda nan take mutum bakwai suka mutu, ɗaya kuma ya samu raunuka.

"Yau rana ce mafi baƙin ciki a rayuwata. Lokacin da aka gaya min cewa ƙasar ta zaftaro ta faɗo musu, nan da nan na garzaya wajen inda na tabbatar da cewa mutum bakwai sun mutu. Wanda ya tsira an kai shi asibiti a Birnin Kebbi."

Kara karanta wannan

Mata Sun Fantsama Kan Tituna, Sun Nuna Fushinsu Kan Kisan Mutum 12 a Bokkos

"Abin baƙin ciki ne a wajena. Ina cikin gida lokacin da wani ya kirani ya gaya min labarin mara daɗi. Har yanzu ji na ke kamar bada gaske ba ne."

- Malam Dan Umar

Gwamnati na shirin ɗaukar mataki

Mai bada shawara ta musamman ga Gwamna Nasir Idris kan jindaɗin Alhazai, Zayyanu Sanka, wanda shi ma ɗan yankin ne, ya yi magana kan lamarin.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta duba yiwuwar haramta ɗebo ƙasa a saman tudun domin hana aukuwar irin haka a nan gaba.

Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa almajirai takwas ne suka rasa rayukansu a sakamakon ruftawar ƙasar.

A kalamansa:

"Eh gaskiya almajirai takwas ne suka rasa ransu sakamakon aukuwar lamarin."

An kashe wata yarinya a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi wa wata yarinya yar shekara 10 mai suna Glory kisan gilla a garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi.

Mahaifiyar yarinyar ta ce yadda aka kasheta ya zo musu da mamaki. Saboda babu wanda ya yi tsammanin za a yi kisan gilla ga yarinya mai wannan shekarun na ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng