Abin da Ba a Taba Yi Ba: Dan Najeriya Ya Kafa Tarihi a Duniyar Wasan ‘Chess’, Tinubu Ya Yaba Masa
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa matasan Najeriya na da juriya da fikira a yunkurinsu na ganin sun taka rawar gani a duniya
- Tinubu, a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi iyakar kokarinta wajen tabbatar da cewa ta himmatu wajen samar da damammaki ga matasan kasar
- Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ya yabawa Tunde Onakoya wanda ya kammala aniyarsa ta kada tarihi a kudin duniya a wasan 'chess' a a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya taya Tunde Onakoya murnar kafa sabon tarihi a duniya tare da nuna jajircewar Najeriya da juriya , da hazakar matasa a duk inda suka tsinci kansu a duniya.

Kara karanta wannan
Shirin zanga zanga a watan Oktoba ya girgiza gwamnatin Tinubu, an fara lallaɓa matasa
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu, ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, Tinubu ya yaba wa Onakoya bisa irin wannan bajintar da ya yi.

Asali: Twitter
Hakazalika, ya yaba masa musamman ganin irin kwarin gwiwar da ke tattare da shi na tara kudade domin tallafawa yara a nahiyar Afirka su koya da kuma samun dama ta hanyar darar ‘chess’.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Al’adar ‘yan Najeriya ne jajircewa, inji Tinubu
Shugaban ya yi nuni da cewa matashin ya nuna al’adar matasan Najeriya ta jajircewa wajen ganin sun samu sauyi mai kyau a fannoni da yawa na rayuwa.
Shugaban buga misalin da Onakoya wajen jinjina wa jajircewar da matasan kasar ke wajen ganin sun tabbatar da sunan Najeriya ya daga a duniya.
A cewar Shugaba Tinubu:
“Matasan Najeriya sun nuna a kowanne fanni, ciki har da wakokin Afrobeats, Nollywood, masana’antu masu tasowa, ilimi, kimiyya, da fasaha, cewa sannu a hankali komai ke girma.”
Tinubu ya tabbatarwa da ‘yan kasar nan cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen fadada samar da damammaki ga matasa don tabuka abin a zo a gani a kasa da ma wajenta.
Yaro dan Najeriya ya fara suna a wasan ‘chess’
Ba wannan ne karon farko ba, a baya kun ji yadda Tanitoluwa Adewumi, wani yaro ne dan Najeriya mai shekaru 8 a duniya, da iyayensa suka tattara su ka koma kasar Amurka ya kafa tarihi a was an ‘chess’.
Yaron, wanda iyayensa suka koma Amurka bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun fitine su, yanzu ya zama abin misali a was an.
Mun rahoto maku yadda yaron a cikin shekaru kadan yak ware a wasan mai bukatar tsananin tunani da mai da hankali.
Asali: Legit.ng