Mata Sun Fantsama Kan Tituna, Sun Nuna Fushinsu Kan Kisan Mutum 12 a Bokkos
- Wasu gungun masu zanga-zanga waɗanda galibi mata ne a karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato sun nuna fushi kan yawan kashe-kashe a yankin
- Sun buƙaci a gaggauta kama maharan da ke aikata wannan ɗanyen aiki kuma a gurfanar da su domin su girbi abin da suka shuka
- Legit Hausa ta tattaro cewa ɗaruruwan mutane aka kashe sakamakon rikicin da ke faruwa a kai a kai a jihar Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bokkos, jihar Filato - Mata a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato sun fantsama kan tituna kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga a garuruwansu.
Kamar yadda Punch ta kawo a rahoto ranar Jumu'a, 19 ga watan Afrilu, fusatattun matan sun zarce kai tsaye zuwa hedkwatar ƙaramar hukumar domin nuna damuwarsu.
Masu zanga-zangar sun nuna matuƙar fushinsu kan ƙaruwar hare-haren rashin imani a ƙaramar hukumarsu ta Bokkos da kuma ƙaramar hukumar Mangu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane 12 mafi akasarinsu mata ne aka kashe haka kawai a ƙauyen Tilengpat da ke yankin Pushit a Mangu ranar Alhamis da ta shige.
Wani shugaban al'umma a Pushit wanda ya faɗi sunansa da John a taƙaice, ya ce:
"Zuwa yanzu mun gano gawarwakin mutum 12 waɗanda aka yi wa gisan gilla yayin harin."
Filato ta faɗi waɗanda take zargi
Marcus Artu, kantoman ƙaramar hukumar Mangu ya bayyana harin a matsayin wani yunƙurin miyagun mutane da nufin ruguza ƙoƙarin gwamnati na mayar da ƴan gudun hijira gidajensu.
Channels tv ta ruwaito Mista Artu na cewa:
"Na zo kauyen domin na yi magana da mazauna kuma na kira taron gaggawa da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin gujewa kai harin ɗaukar fansa da karya doka da oda."
Legit Hausa ta fahimci cewa an ƙara tura jami'an tsaro zuwa ƙauyukan da lamarin ya afku domin tabbatar da zaman lafiya.
An sace kusan mutum 50
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane a kauyukan kananan hukumomin Batsari da Malumfashi a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa kusan mutum 50 ciki har da mata da ƙananan yara ƴan bindigar suka sace a kauyuka 3 cikin wannan makon.
Asali: Legit.ng