'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta, Sun Kashe Bayin Allah Sama da 20 a Kaduna
- Ƴan bindiga sun kashe mutane akalla 23 yayin da suka kai sabon farmaki a kauyen Anguwar Danko da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a Kaduna
- Wani shugaban al'umma ya bayyana yadda ƴan bindigan suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi ranar Laraba da daddare
- Har kawo yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda jihar kan wannan sabon hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ƙaduna - Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 23 ne suka rasa ransu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki kauyen Anguwan Danko a jihar Kaduna.
Garin dai na kusa da Dogon Dawa a gabashin ƙaramar hukumar Birnin Gwari wadda ta haɗa boda da jihar Katsina a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sai dai har kawo yanzu rundunar ƴan sanda da gwamnatin Kaduna ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da harin ba, Premium Times ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya faru
Amma wani shugaban al'umma a kauyen, Zubairu Abdulrahuf, ya shaida wa Channels tv cewa ƴan bindiga masu yawa ne suka shiga garin da daren ranar Laraba.
Abdulrahuf ya bayyana cewa daga zuwan maharan, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutanen ƙauyen.
A cewarsa, yayin haka ne ƴan bindigar suka kashe mutane sama da 20 a mummunan harin da suka kaddamar kan waɗanda ba su ji ba kuma ba su gani ba.
Ya ƙara da cewa bayan yawan mutanen da suka mutu sakamakon harin ta'addancin, wasu mutum biyar sun sami raunuka daban-daban na harbi.
Zubairu Abdulrahuf ya ce har yanzu akwai mazauna kauyen da suka ɓata babu wanda ya san inda suka shiga duk sanadin harin na ranar Laraba da daddare.
Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda ƴan bindigar suka shiga Anguwar Danko, suka fara yinkurin garkuwa da mutane.
Jihar Kaduna dai na ɗaya daga cikin jihohin da ta'addancin yan bindiga ya fi yi wa illa, kuma har yanzun mahukunta sun gaza kamo bakin zaren.
An kama ƴan daba a Kano
A wani rahoton kuma Wasu ƴan daba sun yi yunkurin kawo hargitsi a bikin rantsar da sabbin kwamishinoni ciki har da ɗan Kwankwaso a fadar gwamnatin Kano.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar cafke su ba tare da sun cimma burinsu ba.
Asali: Legit.ng