Ribadu Ya Fadi Irin Gatan da Tinubu Ya Yi Wa Arewa Fiye da Yankinsa, Ya Kawo Dalilai
- An bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya fi kowa son yankin Arewacin Najeriya fiye da sauran yankuna
- Mai ba shugaban shawara a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu shi ya bayyana haka a jihar Sokoto a yau Laraba 18 ga watan Afrilu
- Legit Hausa ta tattauna da jigon jami'yyar APC a Gombe kan wannan magana da Nuhu Ribadu ya yi kan muƙamai a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mai ba da shawara kan harkar tsaro ga Shugaba Bola Tinubu, Nuhu Ribadu ya bayyana irin gatan da shugaban ya yi ga Arewa.
Ribadu ya ce Tinubu ya zabi wasu mukamai masu muhimmanci ya ba yankin domin tabbatar da dakile matsalolinta, cewar Daily Trust.
Wane korafi Ribadu ya yi kan Arewa?
Hadimin ya bayyana haka ne a yau Alhamis 28 ga watan Afrilu a Sokoto inda ya ce shugaban ya san matsalolin yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka kan yadda yankin Arewa ke fama da matsalolin tsaro da yaran da basu zuwa makaranta da sauransu.
Ya kara da cewa talaucin da ke yankin ya yi ƙamari wanda ya ke kawo cikas ga al'umma a Arewa, cewar Daily Post.
Ribadu: Mukaman da Tinubu ya ba Arewa
"Lokacin da Tinubu ya ke haɗa gwamnatinsa, ya bayyana cewa ya na matukar kaunar Arewa a zuciyarsa."
"Ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa domin ganin ya dakile matsalolin yankin a cikin kankanin lokaci."
"Shiyasa ya bamu mukamai masu kyau, ya bamu ministan tsaro da noma da kuma ilimi, sannan ministan harkokin waje da kuma lafiya."
- Nuhu Ribadu
Ribadu ya ce Tinubu ya ba 'yan Arewa mukamai ya kamata a kawar da dukkan bambance-bambance domin kawo ci gaba a yankin, cewar rahoton Naija News.
Martanin jigon APC kan lamarin
Legit Hausa ta tattauna da jigon jami'yyar APC a Gombe kan wannan magana ta Nuhu Ribadu
Hon. Muhammad Auwal Akko ya ce tabbas haka ne Shugaba Tinubu ya ba 'yan Arewa mukaman da suka dace da matsalolinsu.
"Tabbas shugaban kasa ya ba da mukamai a Arewacin Nijeriya wadanda suka shafi matsalolin yankin."
"Matsalolin Arewa ba su wuce Ilimi da tsaro da noma da inganta rayuwar matasa da sauransu ba."
"Amma ba a nan gizo ya ke sakar ba, dukkan wadannan ministoci yan Arewa fa ba zasu samu nasarar aiwatar da abin da ake so ba tare da kudi ba, sannan dukkan ministoci masu kula da harkar kudi ya kai su Kudu."
"Don haka sai in shi kansa ya na da muradin taimakon Arewa kafin wadannan ministocin namu su samu damar yin abin da ya dace."
- Hon. Muhammad Abubakar Akko
Tinubu ya yabawa Dangote kan rage farashi
Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa attajiri Aliko Dangote kan rage farashin litar dizal a Najeriya.
Tinubu ya ce rage farashin zai yi matukar kawo ci gaba a kasar da kuma dakile tashin kayayyaki da ake fama da shi.
Asali: Legit.ng