Ba Za Mu Yarda Ba, Dattawan Arewa Sun Soki Hari Kan Mutanensu a Yankin Kudu
- Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta mayar da martani mai zafi a kan yawaitar kai hare-hare kan 'yan Arewa mazauna Kudu da dukiyoyinsu
- Dattawan sun yi martanin ne biyo bayan wani fai-fan bidiyo da ke nuna wasu mazauna Kudu suna kai hari kan shanun 'yan Arewa da ke wajen gida
- Legit ta tattauna da wani dan Arewa mai hada-hada a Kudu domin jin irin halin da suke shiga da matakan da suke dauka idan an kai musu hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Kungiyar dattawan Arewa ta mayar da martanin a kan zargin sabon salon cin zarafin 'yan Arewa mazauna Kudu.
Kungiyar ta ce ana samun yawaitan kai hare-hare kan shanu da 'yan Arewa masu gudanar da sana'o'i a Kudu musamman a kudu maso gabas.
Jaridar Tribune ta ruwaito mataimakin darakta janar na kungiyar, Salisu Muhammad, yana cewa lalle ba za su yarda da cigaba da yiwa 'yan Arewa kisan gilla da wulakanci ba saboda kawai sun zabi zama a Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya jawo martanin dattawan Arewa
A wani rahoton da jaridar Leadership ta ruwaito ya nuna martanin ya biyo bayan wani faifayin bidiyo ne da ya nuna wasu mazauna Kudu suna kashe shanun 'yan Arewa.
Kiran kungiyar dattawan Arewa ga Bola Tinubu
Kungiyar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmad Tinubu da ya kara himma wajen ganin kawo karshen hare-haren babu gaira babu dalili da wasu bata gari ke kaiwa kan 'yan Arewa a Kudu.
NEF ta na mai cewa hare-haren zai kai ga koma baya wurin kiran da ake domin dunkulewan 'yan Najeriya wuri ɗaya.
Ta kara da cewa babu wani dalili da za a rika zage-zage a kan wadanda suka zabi yin sana'o'in halal a Kudu balle ma ace za a kashe su.
Jawabin dan Arewa mazaunin Kudu
A hirar da Legit ta yi da Muhammad Adamu, wani dan Arewa mazaunin Kudu, ya ce a cikin shekaru 5 da ya shafe yana hada-hada a yankin, ya ga tsangoma da nuna wariya wa mutanen Arewa sosai.
A cewarsa, wani lokacin masu shaguna suna kara musu farashin kayayyaki a kan yadda mutanen gari ke saya.
Ya labartawa Legit cewa akwai lokacin da aka kona musu sabbin motoci a Abba saboda ƙabilanci. A wasu lokutan kuma, ya ce idan motarsu za ta wuce sai ace sai sun biya haraji.
Dan gane da mataki da suke dauka kuwa, Malam Muhammad ya ce idan aka farwa 'yan Arewa, sai dai su gudu su bar dukiyarsu saboda hukuma ba ko yaushe suke zuwa a kan lokaci ba.
Game da kiran da dattawan Arewa suka yi kuwa, Muhammad ya yabawa ƙoƙarin, amma kuma ya kara da cewa dole ne ya zama sun dage da magana a ko da yaushe ba wai lokacin bayan lokaci ba.
An koka kan kisan 'yan Arewa a Kudu
A wani rahoton kuma, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta koka kan yada ake samun yawaitar kisan 'yan Arewa a Kudu.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnati, jimi'an tsaro da sauran kungiyoyi wurin su dukufa wurin kare rai da dukiyar 'yan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba.
Asali: Legit.ng