Hukumar EFCC Ta Yi Barazanar Hada Kai da Sojoji Domin Kamo Tsohon Gwamnan APC

Hukumar EFCC Ta Yi Barazanar Hada Kai da Sojoji Domin Kamo Tsohon Gwamnan APC

  • Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ba ta ji daɗin yadda tsohon gwamnan Kogi yake wasan ɓuya da ita ba
  • EFCC ta hannun lauyanta ta yi barazanar yin amfani da sojoji domin kamo Yahaya Bello ya fuskanci shari'a a gaban kotu
  • Jami'an EFCC sun kai samame a gidan tsohon gwamnan da ke birnin tarayya Abuja, amma ba su yi nasarar kama shi ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta yi barazanar yin amfani da sojoji wajen kamo tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, daga inda yake ɓoye.

Hukumar EFCC da tsohon gwamnan sun yi ta wasan ɓuya a makonnin da suka gabata a ƙoƙarin da ganin an cafke shi.

Kara karanta wannan

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan rikicin Yahaya Bello da EFCC

EFCC na son cafke Yahaya Bello
Hukumar EFCC na son gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello, EFCC
Asali: Facebook

Hukumar ta kai samame a gidan Yahaya Bello da ke Abuja ranar Laraba domin kama shi, amma ta kasa yin hakan saboda wasu da suka shiga tsakani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis ɗin nan ne ya kamata a gurfanar da Bello a gaban kotu amma hakan bai samu ba saboda rashin zuwansa, cewar rahoton Pulse.ng

Barazanar da EFCC ta yi wa Yahaya Bello

Jaridar Leadership ta ce a yayin zaman da aka yi a ranar Alhamis, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, ya shaida wa kotu matsayarsu.

Hukumar za ta gurfanar da Yahaya Bello domin ya fuskanci shari’a, ko da kuwa hakan na nufin amfani da sojoji domin su kamo shi.

"Wataƙila mu gayyaci sojoji domin fitar da Yahaya Bello daga inda yake ɓoye."
"Wataƙila mu yi amfani da sojoji domin fito da shi da ƙarfin tuwo saboda a inda yake ɓoye ba shi da kariya."

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

"Ba wanda ya fi ƙarfin doka. Gwamnan ne kawai yake da kariya ba kowa da yake tare da shi ba."

- Kemi Pinheiro

EFCC ta aikawa Yahaya Bello gargaɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta yi gargaɗin cewa ba za ta sake lamuntar wani ya kawo mata cikas a ayyukanta ba.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya yi gargaɗin cewa babban laifi ne daƙile jami'an hukumar daga gudanar da aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng