Wawure N80bn: EFCC Za Ta Gurfanar da Tsohon Gwamna da Wasu Mutum 3 a Gaban Kotu

Wawure N80bn: EFCC Za Ta Gurfanar da Tsohon Gwamna da Wasu Mutum 3 a Gaban Kotu

  • Hukumar EFCC za ta gurfanar da Yahaya Bello da sauran mutum uku da ake tuhuma a gaban kotun tarayya mai zama a Abuja
  • Wannan na zuwa ne yayin da jami'an hukumar suka gamu da cikas a kokarin cafke tsohon gwamnan jihar Kogi a gidansa
  • Ranar Alhamis, tawagar lauyoyin EFCC za su gurfanar da waɗanda ake zargi kan tuhume-tuhume 19 na wawure N80bn

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello ranar Alhamis, 18 ga Afrilu, 2024.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

Kara karanta wannan

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan rikicin Yahaya Bello da EFCC

Alhaji Yahaya Bello.
EFCC z ata gurfanar da Yahaya Bello da wasu mutum 3 a babbar kotun tarayya Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Za a gurfanar da shi a gaban mai shari’a Emeka Nwite tare da wasu mutane uku da ake tuhuma, Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuhume-tuhumen EFCC a kan Yahaya Bello

Hukumar ta maka Bello da sauran mutane uku a gaban ƙuliya ne bisa wasu tuhume-tuhume 19 da suka shafi karkatar da kudi har N80, 246,470, 088.88.

Shirin gurfanar da tsohon gwamnan na zuwa ne bayan kotun tarayyar ta amince EFCC ta cafke Yahaya Bello domin ya fuskanci shari'a.

Dukkan waɗanda ake zargin za su fuskanci shari'a kan tuhume-tuhume 19 da suka ta'allaka a kan laifin zamba a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CR/98/2024.

Babban lauya a Najeriya (SAN), Dakta Kemi Pinheiro ne ya shigar ƙarar a gaban kotun ranar 6 ga watan Maris, 2024.

Pinheiro da wasu da suka kai matsayin SAN su biyu, Jubrin Okutepa da Rotimi Oyedepo, sune za su jagoranci lauyoyi bakwai na EFCC kan wadanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

A tuhuma ta 18, an zargi Bello da sa wani kamfani ya tura jimlar kudi dalar Amurka 570,330.00 zuwa wani asusu a bankin TD na kasar Amurka.

Hukumar EFCC ta gaza kama Bello

Yunkurin da jami'an EFCC suka yi na kama Yahaya Bello ya fuskanci turjiya a ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2024.

Gwamnan jihar Kogi na yanzu Usman Ododo ya fasa jami'an da suka kewaye gidan tsohon gwamnan da ke Abuja kuma ya tabbatar da sun tafi tare a motarsa.

...EFCC ta yi gargaɗi na musamman

A wani rahoton kuma hukumar EFCC ta gargaɗi duk wani mai kokarin daƙile yunkurin jami'anta yayin gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada.

Wannan gargaɗi da jan kunne na zuwa ne yayin da Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya daƙile yunkurin cafke Yahaya Bello a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262