Tinubu Ya Magantu Bayan Dangote Ya Rage Farashin Mai, Ya Ja Hankalin 'Yan Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yabawa attajiri Aliko Dangote kan rage farashin litar mai a matatarsa
- Tinubu ya ce wannan mataki da attajirin ya ɗauka zai tabbatar da rage farashin kayayyaki a Najeriya a halin da ake ciki
- Hakan ya biyo bayan rage farashin litar man daga N1,200 zuwa N1,000 da matatar ta yi ga al'ummar Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi martani bayan Aliko Dangote ya rage farashin litar mai.
Tinubu ya yabawa attajirin bayan ya rage farashin litar dizil daga N1,200 zuwa N1,000 i ya ce hakan zai taimaka wurin rage farashin kaya.
Nawa Dangote ya rage a farashin dizil?
Wannan na zuwa ne bayan rage farashin daga N1,650 zuwa N1,200 watanni uku da suka wuce kafin sake rage shi a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Batun na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren hulda da jama'a, Fredrick Nwabufo ya fitar.
Nwabufo ya bayyana haka ne a yau Laraba 17 ga watan Afrilu a shafinsa na X inda ya ce Tinubu ya ji dadin lamarin.
Shugaban ya ce ragin wanda ya kai kaso 60% zai taimaka wurin rage farashin kayayyaki a ƙasar.
"Shugaba Tinubu ya tabbatar cewa 'yan Najeriya da harkokin kasuwancin cikin gida sune hanyoyi mafiya sauki wurin inganta tattalin arzikin kasar."
"Ya ce saka hannu na kaso 20 a kamfanin Dangote da yarjejeniyar da aka yi zai taimaka wurin inganta rayuwar 'yan kasar baki daya."
- Bola Tinubu
Wace shawara Tinubu ya ba 'yan Najeriya?
Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su tabbatar sun mayar da hankali wurin ci gaban kasar baki daya.
Ya kara da cewa zai ba da dukkan gudunmawa wurin ba da yanayi mai kyau domin samun abin da ake nema.
Dangote ya rage farashin litar mai
A baya, mun kawo muku labarin cewa matatar man Dangote ta dauki mataki kan farashin litar dizil a Kamfanin.
Matatar ta Dangote ta rage farashin litar mai din ne daga N1,200 zuwa N1,000 domin saukakawa al'umma.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Lahadi 14 ga watan Afrilun da muke ciki.
Asali: Legit.ng