Bola Tinubu Ya Kaddamar da Sabon Tsarin Zamani, Za a Adana Biliyoyin Dalolin Kuɗi
- Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon tsarin aiki wanda zai rage asarar makudan kuɗin shiga a Najeriya duk shekara
- Shugaban ƙasar ya ce Najeriya za ta ceto $4bn a kowace shekara ta hanyar rage ayyukan ofis da toshe hanyoyin cin hanci da rashawa
- Tsarin aikin wanda aka raɗawa suna, "Single Window" wani shafin yanar gizo ne da zai sauƙaƙa harkokin kusuwanci a ciki da wajen ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu a ranar Talata ya ce Najeriya na shirin cin gajiyar kusan dala biliyan 2.7 a duk shekara ta hanyar aiwatar da tsarin aikin 'Single Window Project'.
Tinubu ya ce aikin zai ceto dala biliyan 4 da ake asara duk shekara sakamakon sarkakiyar ma’aikatu da cin hanci da rashawa da ke kawo cikas ga ci gaban kasuwanci.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kaddamar da sabon tsarin kasuwanci na zamani, wanda aka raɗawa suna, "National Single Window project" a fadar Aso Villa, Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da sabon tsarin ya ƙunsa?
Wannan tsarin dai wani shafin yanar gizo ne wanda zai sauƙaƙe kasuwanci ta hanyar haɗa ƴan kasuwar mu na gida Najeriya na kasashen waje a shafi ɗaya.
Shafin yanar gizon zai ba ƴan kasuwar Najeriya da na duniya damar samun isassun kayan aiki da duk abin da suke buƙata daga hukumomin Najeriya daban-daban.
Bola Tinubu ya ce shirin zai kara habaka safarar kayayyaki ta ruwa da kuma inganta kasuwanci tsakanin kasashen Afrika, wanda za a iya cinikin $2.7bn ba tare an yi amfani da takarda ba.
Shugaban kasar ya kara da cewa Najeriya ba za ta lamurci ci gaba da asarar kuɗi har $4bn a kowace shekara ba, rahoton Channels tv.
Najeriya ta shiga sahun manyan ƙasashe
Ta haka ne Najeriya za ta shiga sahun kasashen Singafo da Koriya da Kenya da kuma Saudiyya wadanda suka samu ci gaba sosai a fannin kasuwanci bayan aiwatar da tsarin nan na kafa guda.
"Ba zamu ci gaba ana rasa kimanin $4bn duk shekara ba saboda bin wasu matakai, jinkiri da cin hanci da rashawa a tashohin mu na jiragem ruwa ba," in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa wannan tsarin zai toshe hanyoyin sulalewar kuɗin shiga kuma ya taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci.
Ɗangote ya karya farashin dizal
Mun samu rahoton cewa za a samu sauƙi a Najeriya yayin da matatar man hamshaƙin attajirin nan Aliko Dangote ta sanar da sake karya farashin man dizal.
Sabon farashin na yanzu ya koma N1000 kan kowace lita saɓanin yadda ake siyar da shi a kan N1200 a makonnin da suka gabata.
Asali: Legit.ng