Jerin manyan ‘Yan kasuwan da su ka fi kowa dukiya a Najeriya

Jerin manyan ‘Yan kasuwan da su ka fi kowa dukiya a Najeriya

- Za ku ji su wanene manyan masu kudin Kasar nan a yanzu

- A jerin mun kawo maza ne kurum ba tare da ambata mata ba

- Dangote wanda ya taka sama da Biliyan 12 shi ne kan gaba

A halin yanzu mun shiga maganar dukiya inda mu ka kawo maku jerin manyan masu kudin Najeriya da babu kamar su a cikin maza ‘yan kasuwa.

Jerin manyan ‘Yan kasuwan da su ka fi kowa dukiya a Najeriya
Aliko Dangote ya fi kowa dukiya a Najeriya da ma Afrika

1. ALIKO DANGOTE

Na farko har gobe a jerin shi ne Aliko Dangote wanda kusan shekaru 10 da su ka wuce ya shiga wannan sahu. Dangote ya ba fiye da Dala Biliyan 12 baya yanzu a Duniya. Dangote yana harkar siminti ne da kayan abinci kuma yana shirin shiga harkar mai.

KU KARANTA:

2. Mike Adenuga

Wanda ke bin bayan Dangote mai shekaru 61 a Duniya shi ne babban Abokin sa Mike Adenuga. Adenuga wanda kusan shi ne na 5 ma a Afrika ya ajiye abin da ya haura Dala Biliyan 5 a asusun sa. Adenuga yana harkar mai ne da kamfanin sadarwa na GLO.

3. Femi Otedola

Femi Otedola yana cikin ‘Ya ‘yan tsohon Gwamnan Legas Michael Otedola. Otedola shi ne Shugaban Kamfanin man nan na Forte Oil Plc da kuma Zenon. ‘Dan kasuwan yana cikin masu shigo da mai Najeriya kuma ya ba Dala Biliyan 2 baya a yanzu.

Idan dai kuma ana maganar Mata masu kudi a Kasar nan, dole a sa irin su Folorunsho Alakija wanda tana ma cikin matan da su ka fi arziki a Duniya. Ana tunani Alakija ta fi Femi Otedola kudi nesa ba kusa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng