Kano: Ana Fargabar Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Barkewar Sabuwar Cuta

Kano: Ana Fargabar Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Barkewar Sabuwar Cuta

  • An samu ɓullar wata baƙuwar cuta wacce ta salwantar da rayukan mutane a ƙauyen Gundutse da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano
  • Ma'aikatan lafiya a ƙauyen sun bayyana cewa an samu rahoton rasuwar mutum 20 sakamakon ɓarkewar cutar wacce ba a san musabbabinta ba
  • Sai dai, shugaban riƙo na ƙaramar hukumar da kansilan ƙauyen sun bada mabambantan alƙaluma kan adadin mutanen da suka rasu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Kimanin mutum 45 ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar wata cuta a ƙauyen Gundutse da ke ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa galibin waɗanda lamarin ya ritsa da su da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi, sun nuna alamun cutar zazzabin cizon sauro, gudawa, da amai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi sabuwar ta'asa ta kashe mutane a jihar Kaduna

Wata bakuwar cuta ta barke a Kano
Bakuwar cuta ta salwantar da rayukan mutum 45 a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Yaushe cutar ta ɓulla a Kano

Abu Sani, wani mazaunin garin da ya rasa yara biyu, ya ce tun farko ƴan uwansa sun yi tunanin zazzabin cizon sauro ne ke damun ɗansa ɗan shekara biyu, wanda ya rasa ransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata mata mai suna Hajara Abubakar, wacce ta kai ɗanta wani asibitin yankin domin yi masa magani, ta bayyana cewa:

"Sama da makonni biyu mutane ke mutuwa a nan sakamakon cutar da ba mu san komai a kanta ba. Ya zuwa yanzu, na san mutane 40 da suka mutu.”

Jami’an lafiya a asibitin na Gundutse sun shaida wa wakilin jaridar a ziyarar da ya kai cewa kawo yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 20.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan lafiya a asibitin, wanda ya so a sakaya sunansa, ya ce tuni suka kai rahoton faruwar lamarin ga ma’aikatar lafiya ta jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki hedkwatar ƙaramar hukuma, sun tafka ɓarna

Ya ce an ɗauki samfurin ruwa da jini domin yin gwaje-gwaje da sanin ainihin musabbabin ɓarkewar cutar.

Mai hukumomi suka ce kan lamarin?

Shugaban riko na ƙaramar hukumar Kura, Yahaya Tijjani Kura, ya tabbatar da ɓarkewar cutar amma ya musanta adadin waɗanda suka mutu, inda ya ce yara uku ne suka rasu.

Sai dai, kansila mai wakiltar Gundutse, Dauda Abdulhamid Gundutse, ya bayyana mutuwar yara uku zuwa biyar yayin da ake ci gaba kula da sauran waɗanda cutar ta kama.

Duk da waɗannan mabanbantan bayanan, a ziyarar da wakilin jaridar ya kai maƙarbartar garin tare da wasu mutane, ya ci karo da sababbin ƙaburbura 35 da suka haɗa da na ƙananan yara guda shida, wanda ya sabawa alkaluman da hukumomi suka bayar.

Da aka tuntubi kwamishinan lafiya na jihar Kano, Abubakar Labaran Yusuf, ya ce har yanzu bai samu rahoto a hukumance daga jami’an lafiya na ƙaramar hukumar ba.

Sai dai, ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan matan Chibok suka dawo da yara 34 bayan Boko Haram sun sako su

Cutar lassa ta ɓulla a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da ɓullar cutar zazzabin lassa a ƙananan hukumomi bakwai na jihar.

Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Bauchi, Toro, Kirfi, Tafawa Balewa, Dass, Ganjuwa da Alkaleri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng