El-Rufai Ya Yi Wa Gwamnoni Fallasa, Ya Bayyana Hanyar da Suke Bi Wajen Tafka Magudin Zabe

El-Rufai Ya Yi Wa Gwamnoni Fallasa, Ya Bayyana Hanyar da Suke Bi Wajen Tafka Magudin Zabe

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi magana kan nasarar da ya samu wajen gudanar da zaɓe ta hanyar amfani da na'ura
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa gwamnoni na amfani da hukumomin zaɓe na jihohi wajen gudanar da maguɗin zaɓe
  • El-Rufai ya yi kira da a soke hukumomin zaɓe na jihohi domin a cewarsa hukumar INEC za ta iya gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa gwamnoni na amfani da hukumomin zaɓen jihohi wajen yin maguɗi.

Jaridar Leadership ta ce El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Maiduguri, a wani taron ƙarawa juna sani na inganta ƙarfin aiki ga manyan jami’an gwamnatin Borno.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban majalisa ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC

El-Rufai ya fadi hanyar magudin zabe
El-Rufai ya ce gwamnoni na amfani da hukumomin zabe na jihohi domin yin magudi Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Gwamnatin Borno ce dai ta gayyaci El-Rufai domin ya gabatar da jawabi a wajen taron ƙarawa juna sanin da ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya tuno da nasarar da ya samu ta hanyar amfani da na’ura a zaɓen ƙananan hukumomin da ya gudanar a lokacin da yake gwamna.

Ya kuma bayyana yadda wani gwamnan jihar Arewa maso Yamma ya so ya yi amfani da irin tsarinsa, amma daga baya ya je ya rubuta sakamako kawai bayan an yi masa cikakken bayani kan yadda ake aiki da na'urar wajen zaɓen.

El-Rufai yana so a soke hukumar zabe?

Tsohon ministan wanda ya bayyana cikakken goyon bayansa kan soke hukumomin zaɓe na jihohi, ya jaddada cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na iya gudanar da dukkan zaɓukan ƙananan hukumomi.

"A lokacin da nake gwamnan jihar Kaduna, na ɓullo da tsarin kaɗa kuri’a ta hanyar amfani da na’ura, na gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ita."

Kara karanta wannan

Ana kishin kishin din zai sauya sheka, El-Rufai ya ziyarci gwamnan Borno

"Bayan zaɓen, mun rasa kusan ƙananan hukumomi uku zuwa huɗu a hannun ƴan adawa, saboda sahihancin zaɓen."
"Saboda mun yi gaskiya a zaɓen, wasu daga cikin ƴan takarar jam’iyyar adawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyarmu saboda adalcin da muka yi a zaɓen."

- Nasir Ahmad El-Rufai

El-Rufai ya yabi Gwamna Zulum

A wani labarin kuma, kun ji cewa Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a matsayin gwamna mafi nagarta a Najeriya a halin yanzu.

Malam Nasiru El-Rufai ya kuma yabawa salon mulkin Gwamna Zulum wajen sake gina jihar Borno da kuma farfaɗo da tattalin arziƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng