Babban Fasto Ya Hasasho Matsalar da Ke Tunkarar Najeriya, Ya Aika da Sakon Gaggawa Ga Tinubu
- Shugaban cocin INRI Evangelical, Primate Ayodele, ya yi wa Najeriya narko da wani labari mara dadi, duk da ci gaban da Naira ke samu
- A ranar Litinin, 15 ga Afrilu, Ayodele ya ce ya hango wahalar da ke tunkarar Najeriya a yayin da kasar ke kokarin fita daga matsin tattalin arziki
- A wani sako da ya aike wa Bola Tinubu, malamin ya ce dole ne gwamnati ta sauya dabarunta na tattalin arziki idan ba haka ba mutane za su wahala
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Primate Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical, ya ce ya hango wahalhalun da ke tunkarar Najeriya duk kuwa da irin karfin da Naira ke samu yanzu.
A wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, a ranar Litinin, 16 ga Afrilu, Ayodele ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sauya dabarunta na tattalin arziki.
Malamin ya ci gaba da cewa har yanzu gwamnatin da Bola Tinubu ke jagoranta ba tayi abin da ya dace ba wajen magance matsalar tattalin arziki a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Matsalar da ke tunkarar Najeriya" - Ayodele
A cewarsa, ya hango nan gaba kadan al’amura za su kara tabarbarewa a Najeriya yayin da kuma za a samu karin hauhawar farashin kayayyaki, jaridar Tribune Online ta ruwaito.
Ayodele ya ce gwamnati na iya kare faruwar hakan ta hanyar inganta harkar noma da tabbatar da wadatuwar man fetur da kuma tace danyen mai a cikin gida Najeriya.
Ya kara da cewa halin kunci da ‘yan Najeriya ke ciki a yanzu somin tabi ne kawai ma damar gwamnati ba tayi abin da ya dace ba.
"Kokarin gwamnati ya yi kadan"- Ayodele
Jaridar PM News ta rahoto Malamin ya ce:
"Gwamnati ta yi kokari sosai kan daga darajar Naira, ta cancanci a yaba mata. Duk da haka, nan gaba kadan abubuwa za su yi tsada sosai, za a samu hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
"Mafi kyawun abin da gwamnati za ta yi shi ne ta nemi hanyoyin da za mu iya noma da tace man mu a nan gida domin inganta tattalin arziki da noman mu."
Hukumar PCACC na tuhumar Ganduje
A wani labarin kuma, an ji hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen jama’a ta jihar Kano (PCACC) ta shigar da sabbin tuhume-tuhume kan Abdullahi Umar Ganduje.
Legit Hausa ta ruwaito cewa PCACC na tuhumar Ganduje da karkatar da kudaden kananan hukumomi, kudaden asusun ajiya na jihar Kano da dai sauran su.
Asali: Legit.ng