"Akwai Damuwa" Gwamna Sule Ya Jero Kananan Hukumomi 8 da Ke Cikin Babbar Matsala
- Gwamna Abdullahi Sule ya koka kan yadda lamarin tsaro musamman yawaitar garkuwa da mutane a wasu sassan jihar Nasarawa
- Abdullahi Sule ya nuna damuwarsa ne yayin taron majalisar tsaron jihar da ya kira bayan ya dawo daga Umrah
- Ya kuma yabawa jami'an tsaro bisa jajircewarsu, wanda a cewarsa ba don kokarinsu ba da matsalar ta zarce haka muni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun karuwar hare-haren masu garkuwa da mutane a jihar.
Gwamna Sule ya faɗi haka ne yayin wani taron gaggawa na majalisar tsaro da ya gudana a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu, 2024 a Lafiya, babbar birnin jihar Nasarawa.
Sule ya ce ya kira taron gaggawa na tsaro ne domin duba halin rashin tsaron da ake ciki da kuma lalubo hanyoyin magance garkuwa da mutane da sauran ƙalubale.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule ya faɗi dalilin kiran taro
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Abdullahi Sule ya ce:
"Dalilin da ya sa na kira wannan taro shi ne domin mu duba yanayin tsaron jiharmu musamman a lokacin da na tafi ƙasar Saudiyya domin yin Umrah.
"Na shiga damuwa kan yadda ake ci gaba da samun karuwar garkuwa da mutane musamman a kananan hukumomin Keffi, Doma, Lafia, Awe, Obi, Keana, Karu da Nasarawa.
"Haka nan muna ganin yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba musamman a yankunan da ke kewaye da Shegye, Katakpa, da wasu kauyuka a karamar hukumar Toto.
"Ga kuma matsalar rikicin ƙabilanci tsakanin garuruwa daban-daban da ke ta faruwa irin wanda ya faru a yankin Ugede, inda aka kashe mutum ɗaya saboda saɓani kuma a ƙabila ɗaya."
Gwamnan ya yabawa jami'an tsaro
Gwamna Sule ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yarda da rundunar ƴan banga ta kowace ƙabila ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sule ya kuma godewa jami’an tsaro da suka yi aiki tukuru don ganin an dakile matsalolin tsaro a jihar waɗanda ka iya lalacewa fiye da halin da ake ciki.
Asalin matsalar da ta damu Najeriya
A wani rahoton kuma Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce yunwa, cire tallafin mai da hauhawar farashin canji ba su bane matsalar Najeriya.
A wurin taron ƙara wa juna sani a Borno, tsohon gwamnan ya ce gazawar shugabanci ne asalin matsalar da ta damu ƙasar nan.
Asali: Legit.ng