“Akwai Lauje Cikin Nadi”: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Kan Dakatar da Ganduje Daga APC

“Akwai Lauje Cikin Nadi”: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Kan Dakatar da Ganduje Daga APC

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu kan dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga jam'iyyar APC
  • Bashir Ahmed ya ce idan har wannan dakatarwar ta tabbata to abin da ya faru da Adam Oshiohmole ne ke shirin faruwa da Ganduje
  • Sai dai APC reshen jihar Kano ta yi watsi da wannan dakatarwar tare da daukar mataki kan shugabannin jam'iyyar da suka fitar da sanarwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bashir Ahmed, tsohon hadimin tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya magantu kan dakatar da Abdullahi Umar Ganduje da jam'iyyar APC ta yi.

Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan dakatar da Ganduje daga APC
Bashir Ahmed ya ce abin da ya faru da Adam Oshiohmole zai iya faruwa da Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ahmed ya ce idan har wannan dakatarwar ta tabbata, to babu shakka akwai wani lauje cikin nadi kuma abin da ya faru da Adam Oshiohmole ne zai faru da Ganduje.

Kara karanta wannan

Tuhumar rashawa: Jam'iyyar APC ta dauki mataki mai tsauri kan Abdullahi Ganduje

APC: Me dakatar da Ganduje yake nufi?

Tsohon hadimin Buhari, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi nuni da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan har an bi ka'idoji a dakatar da shugaban jam’iyyarmu na kasa da ake yadawa an yi, to ba shakka yanzu shi ba dan jam’iyya bane.
"Kuma wannan dakatarwar tana nufin cewa ba zai iya ci gaba da zama shugaban jam'iyyar na kasa ba kamar yadda doka ta tanadar."

Bashir Ahmed ya kara da cewa irin abin da ya faru da Ganduje a yanzu, hakan ta taba faruwa da tsohon shugaban jam'iyyar Sanata Adams Oshiohmole a lokacin da yake kan kujerar.

Ya ce tsige Ganduje wata iriyar dabara ce da aka yi amfani da ita wajen tsige Oshiohmole kuma hakan na nufin akwai wasu a bayan fage da ke kitsa duk abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Rudin soyayya: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da jami'inta ya kashe mace mai ciki

APC ta dakatar da Ganduje

A yau Litinin, 15 ga watan Afrilu ne Legit Hausa ta ruwaito maku cewa jam'iyyar APC reshen gundumar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

Halliru Gwanzo, mai ba wa jam'iyyar shawara kan harkokin shari’a a gundumar ne ya sanar da dakatarwar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano.

"Ba mu dakatar da Ganduje ba" - APC

Sai dai tun ba aje ko ina ba, kwamitin ayyuka na APC reshen jihar Kano ya hukunta wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka dakatar da Umar Abdullahi Ganduje.

Shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Dawakin Tofa, Inusa Dawanau, ya ce wadanda suka yi yunkurin dakatar da Ganduje sun aikata laifin yi wa jam'iyya zagon kasa.

Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto gwamnatin jihar Kano ta yi karar tsohon gwaman jihar Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu biyar kan laifin karbar rashawa.

Tuni dai babbar kotun jihar ta saka ranar Laraba mai zuwa a matsayin ranar fara sauraron shari'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.