“An Yi Hawan Sallah da Shi”: Masarautar Zazzau Ta Yi Babban Rashi, Hakimin Ikara Ya Rasu
- Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa Injiniya Aminu Umar, Hakimin Ikara kuma Walin Zazzau ya rasu
- Shugaban sashen yada labarai na masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar
- Allah ya karbi rayuwar marigayi Injiniya Aminu ne da safiyar jiya Lahadi, 14 ga watan Afrilu bayan gajeriyar jinya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zariya, jihar Kaduna - Rahotanni sun bayyanna cewa Allah ya karbi rayuwar Injiniya Aminu Umar, Hakimin Ikara kuma Walin Zazzau da ke jihar Kaduna.
"Walin Zazzau ya yi hawan Sallah" - Kwarbai
Da yake tabbatar da wannan babban rashi, Abdullahi Aliyu Kwarbai, kakakin masarautar Zazzau, ya ce marigayin ya halarci dukkannin bukukuwan Sallah na bana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwarbai ya ce marigayi Injiniya Umar ya halarci Hawan Daushe da Hawan Daba da aka yi a Zariya a ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Haka zalika ya ce marigayin na daga cikin hakiman da suka kai wa Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli gaisuwar Sallah.
"Wali tsatson Sarkin Zazzau Dalhat ne" - Kwarbai
A cewar sanarwar da Kwarbai ya wallafa a Facebook:
"Allah ya karbi rayuwar marigayi Injiniya Aminu ne da safiyan yau (jiya Lahadi) bayan gajeriyar jinya."
"Ya rasu ne bayan an yi dukkanin bukukuwan Sallah da shi, kuma yana daga cikin hakiman da suka kai wa Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli gaisuwar Sallah."
Marigayi Injiniya Umar ya kasance tsatso ne na marigayi Sarki Dalhat daga kabilar Barebari da suka mulki masarautar Zazzau.
Marigayin ya rasu ne ya bar mata da yara da dama kuma tuni aka yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
An dakatar da Ganduje daga APC
A wani labarin na daban, jam'iyyar APC reshen gundumar Ganduje da ke karamar hukumar Tofa, jihar Kano ta dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga jam'iyyar.
Mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Halliru Gwanzo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.
Gwanzo ya ce jam'iyyar ta dakatar da Ganduje ne saboda tuhumar cin hanci da rashawa da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.
Asali: Legit.ng