Yadda masarautar Zazzau tayi rashin manya biyu; Iyan Zazzau da Talban Zazzau, a ranar guda
- Masarautar Zazzau a ranar Juma'a ta yi rashin manya biyu kuma rana guda.
- Iyan Zazzau, Bashir Aminu, da Talban Zazzau, Abdulkadir Iya-Pate, sun rasu yau Juma'a
Masarautar Zazzau ta yi babban rashin da ba tayi irinta ba tun rasuwar marigayi sarkin zazzau, Alha Shehu Idris.
Manyan masu sarauta biyu suka mutu ranar juma'a.
Yayinda Iyan Zazzau, Aminu, ya rasu a wani asibitin jihar Legas kuma aka kai shi Zaria domin jana'iza, Talban Zazzau, Iya-Pate, ya rasu ne a Zariya bayan rashin lafiyan da yayi fama da shi.
Mai martaba sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, ya fara sanar da mutuwar Iyan Zazzau a shafin Tuwita, ranar Juma'a.
"Cikin bakin ciki da alhini muke sanar da mutuwar mai sarauta mafi karfi kuma Yarima mafi arziki a arewacin Najeriya, Alha Bashar Aminu, Iyan Zazzau," yace.
Iyan Zazzau na daya daga cikin Yaromomin Zazzau da suka nemi kujeran Sarkin Zazzau bayan rasuwar, Alhaji Shehu Idris, amma bai samu nasara ba.
KU KARANTA: Muhimman Abubuwa 5 da Buhari ya fada a jawabinsa na sabuwar shekara
KU DUBA: Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna)
Bayan da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya zabi Ahmed Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 a watan Oktoba, margayi Iyan zazzau ya shigar da kara kotu inda yake kalubalantar nadin Bamalli matsayin sarki.
Iyan zazzau ya bukaci babbar kotun jihar Kaduna dake zaune a Zariya ya kwance rawanin Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 kuma ta sanar da shi a matsayin halastaccen sarki.
Ya bukaci kotun ta yi haka saboda shi majalisar masu zaben sarki suka zaba ranar 24 ga Satumba, 2020.
A zaben da aka gudanar, marigayi Aminu ne ya samu maki mafi yawa, inda ya zarcewa sauran Yarimomin, Yariman Zazzau, Munir Jafaru, na gidan sarautan bare-bari da kuma Turakin zazzau, Aminu Idris, na gidan sarautan Katsinawa.
Ana kyautata zaton cewa mutuwar Aminu zai kawo karshen zaman da ake a kotu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng