Ana Kishin Kishin Din Zai Sauya Sheka, El-Rufai Ya Ziyarci Gwamnan Borno

Ana Kishin Kishin Din Zai Sauya Sheka, El-Rufai Ya Ziyarci Gwamnan Borno

  • Ana kishin kishin din zai sauya sheka, Mallam Nasir El-Rufa'i ya sauka a jihar Borno domin gudanar da wani muhimmin al'amari
  • Wani hadimi ga tsohon gwamnan ya tabbatar da faruwar lamarin ta wata sanarwa a ranar Lahadi, 14 ga Afrilu tare da bayyana dalili
  • ‘Yan Najeriya a soshiyal midiya sun yi martani dangane da faruwar lamarin, wasu na ganin cewa akwai shirin da El-Rufai yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Borno - Yayin da ake sukar gwamnatinsa da kuma jita-jitar sauya sheka, Mallam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya dura jihar Borno a halin yanzu.

El-Rufai ya gana da Gwamna Babagana Zulum a Borno
El-Rufai ya isa jihar Borno domin gudanar da wani muhimmin taro. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Asali: Twitter

Me yasa El-Rufai yaje jihar Borno?

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, tsohon Sanata da ɗan Majalisa sun watsar da PDP, sun koma APC

El-Rufai dai ya je jihar ne domin wata muhimmiyar ganawa da gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muyiwa Adekeye, hadimin El-Rufai kan harkokin yada labarai ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, 14 ga Afrilu, 2024.

Ya yi nuni da cewa tsohon gwamnan zai yi jawabi ne a taron karawa juna sani na gwamnatin jihar Borno.

Adekeye ya wallafa cewa:

"Mai girma Farfesa Babagana Umara Zulum ya tarbi Malam Nasir @elrufai a Maiduguri. Malam @elrufai zai yi jawabi ne a wani taron karawa juna sani na gwamnatin jihar Borno."

'Yan Najeriya sun magantu ziyarar El-Rufai

Legit.ng ta dauko wasu ra'ayoyi na jama'a dangane da zuwan El-Rufai Borno:

@martinokorowu ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, sun tafka ɓarna a jihar Arewa

"Abu ne mai kyau."

@AdamawaLas79384 ya ce:

"Malam yana shirya wani babban abu."

@Zarmaomar ya ce:

"Shugaban tarayyar Najeriya mai jiran gado."

@ibroayo ya ce:

"Mutum mai daraja ne kawai ke iya yin magana a taron karawa juna sani ga mutane masu daraja."

@AuwalBalabakori:

"Har yanzu mutumin yana kan ganiyarsa, Allah ya kara yi wa rayuwa albarka yallabai."

El-Rufai ya shirya fada da Tinubu?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya shirya yin fada da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

KAmar yadda rahotanni suka bayyana, za a yi wannan fadan ne a gaban kotu bayan da El-Rufai ya shirya wanke kansa daga zargin da ake na cewa shi hatsari ne ga tsaron Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.