“N200/L”: Kamfanin Najeriya Ya Gina Gidajen Man CNG, Zai Karya Farashin Man Fetur
- Kamfanin iskar Gas na NIPCO ya ce ya kammala aikin gina gidajen sayar da iskar gas din CNG guda hudu a Legas
- Kamfanin ya bayyana cewa gidajen man za su fara zuba man CNG ga ababen hawa a jihar daga watan Afrilu
- NIPCO ya ce zai rika siyar da CNG ga masu ababen hawa a kan N200/scm idan aka kwatanta da N670/L na man fetur
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kamfanin iskar gas na NIPCO ya kammala ginawa da kuma bude sabbin gidajen sayar da gas din CNG guda hudu a Legas domin karya farashin man fetur.
Za a bude gidajen man guda hudu domin ayyukan kasuwanci a karshen watan Afrilu kuma za su zama na farko a Legas.
CNG ya fi rahusa a kan fetur
A cewar Nagendra Verma, manajan kamfanin gas na NIPCO, kamfanin ya tsunduma cikin harkar kasuwancin gas tun daga 2009.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Leadership ta ruwaito cewa shugaban NIPCO ya bada tabbacin dorewar samar da iskar gas da kuma siyar da shi a kan N200 maimakon N670 da ake siyan man fetur a Abuja.
Verma ya ce ga manyan motoci, za su sayi CNG a kan N260/scm maimakon Naira 1,250 na dizal a Legas da kuma N290/scm na CNG sabanin N1,300 a kan kowace litar dizal a Abuja.
Verma ya ce:
"NIPCO Gas yana da tabbacin cewa la'akari da kokarin gwamnati mai ci na mayar da hankali kan AutoCNG, iskar za ta maye gurbin man fetur a Najeriya nan ba da dadewa ba."
NIPCO ya bude gidajen mai 15 a Najeriya
Ya bayyana cewa CNG mai ne na talakawa kuma yana da mahimmanci ga kasa, yana mai cewa idan kamfanin ya fadada a Najeriya, zai rage masu ababen hawa tsadar man fetur.
Yayin bayyana dabarun kamfanin, jaridar The Guardian ta ruwaito shi yana cewa kamfanin ya fara ne a cikin garin Benin kafin ya fadada harkokinsa na CNG zuwa jihar Ogun da Kogi.
Kamfanin NIPCO yana aiki da tashoshin CNG guda 15 a fadin Najeriya, kuma motocin CNG a Legas na bin hanyar da ke tsakanin tashoshin kamfanin idan za su je Abuja da Kaduna.
IPMAN za ta fara dakon CNG
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa dillalan man fetur na Najeriya sun sanar da cewa suna daf da fara dako da kasuwancin iskar gas din CNG.
A cewar kungiyar, man CNG zai iya maye gurbin man fetur la'akari da cewa ya fi fetur arha kuma baya saurin konewa.
Asali: Legit.ng