Nan da 2022 hawa mota mai amfani da fetur zai fi karfin talaka - shugaban DPR

Nan da 2022 hawa mota mai amfani da fetur zai fi karfin talaka - shugaban DPR

> Hukumar DPR ta sanar da cewa nan bada dadewa ba motoci ma su amfani da sinadarin gas za su koma ma su rinjaye a Najeriya

> Shugaban hukumar DPR, Sarki Auwalu, ya ce motoci ma su amfani da gas za su maye gurbin motoci ma su amfani da man fetur

> Gwamnatin tarayya ta na ganin hakan ne kadai mafita daga matsin da jama'a su ka shiga sakamakon tashin farashin man fetur

Sarki Auwalu, shugaban hukumar kula da cinikayyar man fetur (DPR), ya ce gwamnatin tarayya (FG) ta na da burin maye guraben motoci ma su amfani da man fetur da ma su amfani da sinadarin gas.

A cewar Auwalu, burin FG shine ganin motoci ma su amfani da sindarin gas sun zama ma fi rinjaye a Najeriya nan da wasu shekaru kadan ma su zuwa.

Auwalu ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da kwamitin majalisar wakilai ya ziyarci hedikwatar DPR a Legas.

Ya bayyana cewa ma su hannu da shuni ne kadai za su iya rike mota mai amfani da fetur saboda yanzu haka FG tana aikin mayar da motoci su koma amfani da sindaran gas irinsu LNG (Liquified Natural Gas), CNG (Compressed Natural Gas) da LPG (Liquified Petroleum Gas).

Darektan na DPR ya bayyana cewa motoci masu amfani da Gas za su maye gurbin ma su amfani da fetur saboda gas ya fi sauki da tsafta.

Nan da 2022 hawa mota mai amfani da fetur zai fi karfin talaka - shugaban DPR
Nan da 2022 hawa mota mai amfani da fetur zai fi karfin talaka - shugaban DPR
Source: Twitter

"Ya kamata a ce 'yan Najeriya suna da zabin abinda zasu yi amfani da shi a tsakanin fetur (PMS) da Gas.

DUBA WANNAN: Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG

DUBA WANNAN: Kano: Mutane uku sun mutu sakamakon rushewar wani a gini a Dawanau

"Yin hakan tamkar basu 'yanci ne a bangaren zabin sayen abin da ya ke daidai da aljihunsu.

"Nan da wasu shekaru amfani da man fetur zai koma na ma su hannu da shuni.

"Za a samu saukin kudin mota idan an koma amfani da gas, saboda ya fi fetur araha da tsarki," a cewarsa.

Auwalu ya bayyana cewa tuni DPR ta fara tattaunawa da ma su ruwa da tsaki domin samar da fanfunan sayar Gas a gidajen man fetur.

Ya ce amfani da Gas ba zai tsaya iya kan motoci kadai ba, hatta kamfanoni da bangaren samar da wutar lantarki za su koma amfani da Gas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel