Crypto: Yayin da Darajar BTC Ta Fadi Zuwa $62,000, Wani Matashi Ya Tafka Asarar N1.3bn

Crypto: Yayin da Darajar BTC Ta Fadi Zuwa $62,000, Wani Matashi Ya Tafka Asarar N1.3bn

  • Wani matashi ya yi asarar duk abin da ya mallaka a kasuwar crypto yayin da farashin BTC ya fadi zuwa $62,000 (N74,431,000) a ranar Asabar
  • Tare da yakinin cewa darajar BTC ba zata taɓa faɗuwa ba, matashin ya sayi sulallan PEPE tare da zuba kudinsa gaba daya domin samun riba mai yawa
  • Ba tare da ya yi amfani da dabarar takaita asarar kudi ba, yana kallo dukkanin kudadensa suka bi ruwa sakamakon sabon rikicin Isra'ila da Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani dan kasuwar crypto ya fuskanci mummunar asara har ta $1.14m (N1,368,570,000) a kan Binance sakamakon gaza yin amfani da dabarar takaita asarar kudi.

Farashin BTC ya fadi sakamakon yakin Iran da Ista'ila
Matashin ya rasa gaba daya kudinsa bayan farashin BTC ya fadi. A kula: Hoton mutumin ba shi da alaka da labarin. Hoto: @crptonerd75, Getty Images/Kelvin Murray
Asali: Twitter

Tare da yakinin cewa darajar BTC ba zata taɓa faɗuwa ba, matashin ya sayi sulallan PEPE tare da zuba kudinsa gaba daya da tunanin samun riba mai yawa.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

Kasuwancin 'futures' a kan Binance

Kasuwancin 'futures' a kasuwar crypto yana da babban haɗari kuma ana yin asara ko a samu riba gwargwadon yawan kudin da aka zuba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da matashin cryptonerd75 yake tunanin zai iya samun ribar kudin da ya zuba nunki 3, sai ya zub $1.14m (N1,368,570,000) ya sayi sulallan PEPE, ganin farashin na haurawa sama.

Cryptonerd75 bai yi amfani da dabarar takaita asarar kudi ta 'Stop Loss (SL)' ba. A cewar Binance (SL) wata dabara ce da 'yan cyrpto ke amfani da ita wajen kayyade iya kudin da zasu rasa idan kasuwa ta juya masu baya.

Farashin BTC da rikicin Isra'ila da Iran

Bayan fitar da labarai game da yakin Iran da Isra'ila, darajar BTC ta fadi warwas, kuma hakan ya sanya farashin wasu sulallan ya fadi.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

Kafin ya farga, sai farkawa matashin ya yi ya ga dukkanin kudinsa sun bi ruwa. Ya ce ko dala 1000 (N1,200,500) ba ta yi sauraa asusun bankinsa ba, ya rasa dukkanin kudin da ya mallaka.

A wani rubutu da ya yi daga baya, ya ce ya tsira da dala 180,000 (N216,090,000) saboda Binance ta yi amfani da iya kashi 83 ne na kudinsa ba wai kashi 100 ba.

Duba rubutunsa a kasa:

Najeriya ta ci tarar Binance $10bn

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta ci kamfanin crypto na Binance tarar dala biliyan 10.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasar shawara ta fuskar yada labarai ya ce an ci Binance tarar ne saboda karya dokokin cinikayya na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel