Neja: Yayin da Ya Ke Fama Da ’Yan Daba Kamar Kano, Gwamna Ya Sanya Dokar Ta Baci

Neja: Yayin da Ya Ke Fama Da ’Yan Daba Kamar Kano, Gwamna Ya Sanya Dokar Ta Baci

  • Yayin da jihohin Arewa ke fama da ‘yan daba, Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya dauki matakin dakile matsalar baki daya
  • Gwamnan ya sanya dokar ta baci inda ya umarci jami’an tsaro da kada su daga kafa ga duk wadanda suke kawo cikas a zaman lafiyar jihar
  • Bago ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido ta na ganin irin wannan ayyukan ‘yan daba da ta’addanci na faruwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja – Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya sanya dokar ta baci kan ayyukan ‘yan daba a jihar.

Gwamnan ya umarci dukkan jami’an tsaro da su dauki mummunan mataki kan duk wadanda ke neman ta da zaune tsaye.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin mutuwar jarumar fina-finai, Gwamna ya bukaci tono gawarta daga kabari

Gwamna ya sanya dokar ta baci kan 'yan daba a jiharsa
Gwamna Umar Bago na Neja ya sanya dokar ta baci kan ayyukan 'yan daba. Hoto: Umar Bago.
Asali: Facebook

Alwashin da ya sha kan 'yan daba

Bago ya bayyana haka ne yayin hawan ‘Durbar’ a jihar wanda tsohon gwamnan jihar, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ya shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba zai taba bari a rinka aikata laifuffuka ba a jihar ya na gani inda ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba, cewar Tribune.

Ya kara da cewa ya umarci jami'an tsaro da su dauki mataki kan duk masu kawo tsaiko a zaman lafiyar jihar.

Tsohon gwamna ya yabawa gwamna Bago

A martaninsa, Mu’azu Babangida Aliyu ya yabawa gwamnan inda ya ce ya daga darajar al’adun jihar, cewar FRCN HQ.

Tsohon gwamnan ya ce irin wannan taro zai kara dankon zumunci tsakanin al’ummar jihar da karin zaman lafiya.

Aliyu ya kirayi al’ummar jihar da su hada kai da juna ba tare da bambancin siyasa ko addini ba domin samun ci gaba.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

Abba ya kadu kan sakin ‘yan daba

A baya, kun ji cewa gwamnan jihar Kano ya koka kan yadda aka saki wasu ‘yan daba a jihar da aka cafke a baya kan laifuffuka.

Gwamnan ya zargi jam’iyyun adawa da hannu a cikin sakin hatsabiban ‘yan dabar da suka addabi birnin Kano da kewaye.

Abba Kabir ya sha alwashin daukar mummunan mataki kan wannan matsalar inda ya ce ba zai zuba ido ana ta’addanci a jihar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.