Kungiyoyin Kwadago Sun Gabatar da Mafi Karancin Albashin da Suke So a Biya Ma'aikata

Kungiyoyin Kwadago Sun Gabatar da Mafi Karancin Albashin da Suke So a Biya Ma'aikata

  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun gabatar da mafi ƙarancin albashi da suke so gwamnati ta biya ma'aikata
  • Ƙungiyoyin na TUC da NLC sun cimma matsayar N615,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi da suke ma'aikata su riƙa samu duk ƙarshen wata
  • Wannan matsayar dai tuni suka sanar da gwamnayi bayan sun kammala tattaunawa a tsakaninsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun buƙaci N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a ƙasar nan.

Ƙungiyoyin biyu sun cimma wannan matsayar ne bayan sun kammala tattaunawa a tsakaninsu.

Kungiyoyin kwadago sun fadi mafi karancin albashi
Kungiyoyin kwadago na son a biya ma'aikata N615,000 matsayin mafi karancin albashi @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Na wa NLC ke son a biya ma'aikata?

Jaridar The Punch ta ce wani majiya wanda babba ne a ƙungiyar ƙwadago da ya nemi a sakaya sunansa shi ne ya tabbatar mata da cimma N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da dama sun mutu a wani sabon fada tsakanin mayakan ISWAP da Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar wanda yana cikin kwamitocin da gwamnati ta kafa domin samar da sabon mafi ƙarancin albashin, ya ce kuɗin za su iya ƙaruwa biyo bayan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi.

A kalamansa:

"Mu a NLC da TUC mun miƙawa gwamnati abin da muke buƙata kan mafi ƙarancin albashi wanda shi ne N615,000. Wannan ita ce matsayar TUC da NLC kan batun. Mun sanar da gwamnati hakan."

Jaridar ta ce wani shugaba a ƙungiyar ƙwadagon ya tabbatar mata da cewa NLC da TUC sun amince da N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Da aka tambaye shi ko har yanzu wa'adin ranar, 1 ga watan Mayu da suka bada har yanzu yana nan, sai ya kada baki ya ce:

"Abin da na ke son ku sani shi ne muna yin bakin ƙoƙarinmu. Da NLC da TUC sun cimma matsaya ɗaya, kuma mun sanar da gwamnati."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun saki ɗaliban Taraba bayan biyan makudan kudin fansa

NLC a son a biya ma'aikata N1m

A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar ‘yan kwadago watau NLC na reshen jihar Ogun, Hammed Ademola-Benco, ya tabo batun albashi. K

Hammed Ademola-Benco ya ce ba su canza shawara a kan biyan akalla N1m a kowane wata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng