Bangaren Maza Ko Mata? Hukumar Gidan Yari Ta Fadi Sashen da Za Ta Ajiye Bobrisky

Bangaren Maza Ko Mata? Hukumar Gidan Yari Ta Fadi Sashen da Za Ta Ajiye Bobrisky

  • Daga karshe, hukumar kula da gidajen yari a Najeriya, NCS ta bayyana sashen da za ta ajiye ɗan daudu, Bobrisky a gidan gyaran hali
  • Hukumar ta ce za ta bi shaidar da ta samu daga kotu inda fitaccen ɗan daudun ya tabbatar da cewa shi namiji ne a gaban kotun
  • Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta gurfanar da Bobrisky kan zargin cin zarafin naira da wulakanta ta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya (NCS) ta bayyana sashen da za ta shiga dan daudu, Idris Bobrisky.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan fitaccen ɗan daudun ya bayyanawa kotu cewa shi namiji ne.

Kara karanta wannan

Watanni 2 da maganar komawa APC, Abba ya dauko binciken Ganduje da iyalinsa

Hukumar NCS ta fadi bangaren da za ta ajiye Bobrisky
Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce za ta ajiye Bobrisky a bangaren maza. Hoto: @bobrisky.
Asali: Instagram

Matakin da hukumar ta dauka kan Bobrisky

Wata majiya daga hukumar ta NCS ta bayyana haka ga 'yan jaridu a ranar Juma'a 12 ga watan Afrilu, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

"Tun da ya riga ya bayyana jinsinsa a kotu, dole za mu yi amfani da abin aka gabatar daga kotu."
"Bai kamata ya ji tsoron cin zarafi daga wasu maza ba saboda jami'anmu za su ba shi dukkan kariya da ya ke bukata."

Zargin da ake yi kan Bobrisky

Tun farko, an kama Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky kan zargin cin mutuncin naira Wanda ya sabawa dokar kasa.

Bayan hukumar EFCC ta cafke shi a jihar Legas, Bobrisky ya nemi sassauci inda ya ce bai san hakan laifi ba ne a Najeriya, cewar Vanguard.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotu tare da umartansa ya fayyace jinsinsa, Bobrisky ya fadawa kotun cewa shi jinsin namiji ne, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

"Mun gano inda ya ke", Gwamnati ta yi karin haske kan shugaban Binance da ya tsere

EFCC ta cafke Bobrisky a Legas

A baya, mun baku labarin cewa Hukumar EFCC ta cafke fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.

Hukumar ta dauki matakin ne bayan zargin Bobrisky da watsa takardun naira da kuma cin mutuncinta wanda ta sabawa doka.

Daga bisani, an gurfanar da fitaccen ɗan daudun a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Legas domin daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel