Shugaba Bola Tinubu Ya Sake Ba Dan Arewa Gingimemen Mukami
- An naɗa Injiniya Kabir Musa Umar a matsayin sabon manajan darakta na kamfanin raba wutar lantarki a gidajen gwamnatin tarayya
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da naɗin Umar a matsayin manajan darakta na FHAEDL a wata sanarwa a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilun 2024
- Injiniya Umar ya taɓa zama mataimakin babban manaja a hukumar kula da gidaje ta tarayya (FHA)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon manajan darakta na kamfanin raba wutar lantarki a gidajen gwamnatin tarayya (FHAEDL).
An naɗa Injiniya Kabir Musa Umar (FNSE), ƙwararre a harkar gidaje da kuma samar da makamashi a matsayin sabon manajan darakta na kamfanin.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Juma’a 12 ga watan Afrilun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene babban muƙamin Umar na ƙarshe?
A cewar sanarwar, babban muƙami na ƙarshe da Umar ya riƙe shi ne mataimakin babban manaja a hukumar kula da gidaje ta tarayya.
Sabon manajan daraktan na hukumar FHAEDL ya kasance ƙwararre ne wanda ya yi suna wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Ya yi digirin farko a jami'ar Ahmadu Bello dan ke Zaria, sannan yana da rajista da COREN da FNSE.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
“Kabir Umar, haifaffen jihar Kano zai kawo ƙwarewarsa, ilminsa, gogewarsa da gudunmawarsa a ɓangaren aikin injiniya a kamfanin FHAEDL."
Tinubu ya ba Ali Nuhu muƙami
A baya kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Ali Nuhu a matsayin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.
Naɗin Aliyu na cikin naɗe-naɗen sababbin daraktoci 11 a ma'aikatar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira.
Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabuwar tawagar waɗanda za su jagoranci hukumar kula da almajiri da yaran da ba su zuwa makaranta.
Tinubu ya amince da naɗin Birgediya Janar Lawal Ja'afaru Isah (mai ritaya) a matsayin babban shugaban hukumar ta ƙasa.
Asali: Legit.ng