Ministan Tsaro Ya Caccaki Dattawan Arewa Kan Kalaman da Suka Yi Game da Bola Tinubu
- Matawalle ya caccaki ƙungiyar dattawan Arewa NEF kan kalaman sukar da ta yi wa gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Ƙaramin ministan tsaron ya ce kungiyar ba ta iya tsinanawa Arewa komai, ta zama tamkar nauyi ga ƴan Arewa
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce NEF ba za ta iya dakatar da kudirin tazarcen Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Mohammed Matawalle, ya caccaki kungiyar Dattawan Arewa (NEF) kan sukar gwamnatin da ke kan mulki.
Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana ƙungiyar dattawan da wani nauyi da ya damu ƴan Arewa, wadda ba ta iya wakiltar yankin a kan komai.
Ministan ya yi wannan furucin ne yayin da yake martani kan wata hira da kakakin NEF, Abdul-Azeez Suleiman ya ce Arewa ta yi nadamar zaɓen Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Matawalle ya kira wannan kalamai da dattawan Arewa suka yi a matsayin butulci, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"An ja hankali na kan wata barazana da kungiyar dattawan Arewa ta yi wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda na ɗauke shi a matsayin butulci.
"Abin kunya ne ga tawagar mutane irin wannan da ke neman samun mafaka a siyasa, su zama nauyi da kuma wargaza haɗin kai tsakanin ƴan Najeriya.
"Wannan NEF da kuke gani nauyi ne mara amfani ga ƴan Arewa, ƙungiyar na neman tauye haƙƙin wasu al'umma don kawai ta samu shiga duk da kunyar da ƴan takararsu suka sha a zaɓen 2023."
- Muhammad Bello Matawalle.
NEF ba zata dakatar da Tinubu ba
Ministan ya ƙara da cewa NEF ba ta da ƙarfin da za ta dakatar da nasarar shugaba Tinubu a babban zaɓen 2027, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
"Duk da mutane da yawa sun yi biris da su, ya dace a nuna abin da suke yi na wuce gona da iri kan batutuwan da suka shafi hadin kan ƙasa da na siyasa.
"Ba zasu iya zama su kawo wani hange ko tunani game da makomar Arewa ko Najeriya gaba ɗaya ba," in ji shi.
Tinubu ya kwantar da hankalin mutane
A wani rahoton kuma Duk da ana fama da yunwa da hauhawar farashin kayayyaki, Bola Ahmed Tinubu ya roki ƴan Najeriya su haɗa kai kuma kada su karaya
Shugaban ƙasar ya faɗa wa ƴan Najeriya cewa su kwana da shirin cewa tattalin arziki zai farfaɗo daga nan zuwa watan Disamba, 2024.
Asali: Legit.ng