Yan Bindiga Sun Farmaki Tsohon Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati, Sun Tafka Ɓarna a Jihar Arewa
- Yan bindiga sun kaiwa tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati hari a jihar Benuwai, sun tafi da matarsa da ƴar aiki
- Ganau ya bayyana cewa maharan sun harbi tsohon CoS a hannu kuma sun yi kokarin tafiya da shi amma ya gaza, suka barshi a nan
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Benuwai, Anene ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Ƴan bindiga sun kai hari gonar Terwase Orbunde, tsohon shugaban ma'aikatan tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.
Yayin wannan harin, ƴan bindigar sun yi awon gaba da matar tsohon hadimin gwamnan, Misis Abigail Orbunde, da ƴar aikinsu, Patience Ogute.
An ce su duka ukun sun je duba gonar da ke kusa da makabarta a gefen titin barikin ƴan sanda-Welfare Quarters a garin Makurdi lokacin da maharan suka kai masu hari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Orbunde na ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar APC gabanin zaɓen fitar gwani na zaɓen 2023.
Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Tahav Argezua ya tabbatar da harin da aka kai wa Orbunde tare da sace matarsa da ƴar aiki.
Yadda lamarin ya auku
Wani ganau ya kara shaida wa wakili jaridar Tribune Online cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Juma’a.
“Bayan sun duba aikin ne kwatsam wasu ‘yan bindiga biyar suka farmaki tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tsohon gwamna da matarsa da kuma ‘yar aikin gidan.
"Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Juma’a kuma ‘yan bindigar sun bude wuta tare da harbin Orbunde a hannun damansa, suka tasa su zuwa cikin daji," in ji shi.
Ya kara da cewa ƴan bindigar sun tafi da su ne a kafa amma daga bisani suka saki Orbunde wanda jini ke ta kwarara daga jikinsa har ta kai ga baya iya tafiya.
Bayan maharan sun tafi da matan biyu sun bar tsohon CoS ɗin a nan sai wasu matasa suka ɗauke shi suka garzaya da shi asibiti, The Nation ta ruwaito.
Yan sanda sun tabbatar da labarin
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar yan sanda (PPRO) a jihar, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin.
"Eh, gaskiya ne, DPO da ke kula da yankin ya sanar da ni,” Anene ta fada a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Asabar.
Mutane sun mutu a harin bama-bamai
A wani rahoton Mazauna ƙauyen Kukawa a karamar hukumar Maradun a Zamfara sun yi ikirarin sojoji sun masu ruwan bama-bamai a filin idi ranar Laraba.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin ya zo wucewa sai ƴan bindiga suka buɗe masa wuta bisa haka ya saki bam ɗin da ya shafi fararen hula.
Asali: Legit.ng