Halin Kunci: Kamar Tinubu, Gwamnan PDP Ya Amince da Biyan Kudin Rage Radadi N35,000

Halin Kunci: Kamar Tinubu, Gwamnan PDP Ya Amince da Biyan Kudin Rage Radadi N35,000

  • Yayin da ake ci gaba da shan fama na tsadar rayuwa a Najeriya, gwamnan jihar Bayelsa ya amince da biyan kudin rage radadi
  • Gwamna Douye Diri ya amince da biyan kudin har N35,000 ga ma'aikatan jihar domin rage musu halin kunci da suke ciki musamman a jihar
  • Mataimakin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo shi ya tabbatar da haka ga shugabannin kungiyar TUC a yankin Kudu maso Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Gwamnatin jihar Bayelsa ta dauki mataki kan halin kunci da tsadar rayuwa da ake ciki.

Gwamnan jihar, Douye Diri ya amince da biyan N35,000 ga ma'aikatan jihar domin rage musu halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Ganduje: Yayin da ake cece-kuce, Abba ya fayyace gaskiya kan kafa kwamitin bincike

Gwamnan PDP ya yi abin alheri kamar Tinubu na biyan kudin rage radadi
Gwamna Douye Diri ya yi bajinta kamar Bola Tinubu, zai biya N35,000 na rage radadi. Hoto: Douye Diri.
Asali: Facebook

Musabbabin daukar matakin biya kudin

Mataimakin gwamnan Jihar, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo shi ya tabbatar da haka a jiya Juma'a 12 ga watan Afrilu, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawrence ya yi alkawarin ne yayin da shugabannin kungiyar TUC a yankin Kudu maso Kudu suka kai masa ziyara a birnin Yenagoa na jihar.

Ya ce daukar wannan mataki na daga cikin bin umarnin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da biyan kudin domin rage radadi ga jama'a.

Wane umarni gwamnan jihar ya bayar?

Har ila yau, Lawrence ya umarci shugabar ma'aikatan jihar, Biobelemoye Charles-Onyeama ta fitar da tsare-tsare domin tabbatar da biyan kudin da gaggawa.

Mataimakin gwamnan ya ce ma'aikata su ne ginshikin aiwatar da duk wasu tsare-tsaren gwamnati a kasar, cewar rahoton The Guardian.

Ya ba da tabbacin cewa Gwamna Diri zai ci gaba da tabbatar da walwalar ma'aikata domin samun kwarin gwiwar ci gaba da ayyukansu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi babban alkawari ga 'yan Najeriya kan halin matsin tattalin arziki a kasar.

Tinubu ya tabbatar da cewa daga nan zuwa karshen shekara da muke ciki komai zai dawo dai-dai ba tare da matsala ba.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke cikin wani irin mawuyacin hali na matsin rayuwa a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.