Mun Dauki Matakan Saukar da Farashin Gas, Cewar Ministan Mai
- Karamin ministan mai, Obongemem Ekpo, ya yi wa 'yan Najeriya albishir da cewa farashin iskar gas zai sauko kwanan nan
- Ministan ya bayyana haka ne wata tattaunawa da yayi da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Abak ta jihar Akwa Ibom
- Ya kuma lissafo matakan da suka riga suka dauka domin ganin farashin gas din ya sauko dai-dai da aljihun talaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Karamin ministan mai, Obongemem Ekpo, ya yi hasashen yiwuwar faduwar farashin iskar gas a Najeriya.
Ministan ya ba da wannan tabbacin ne a wani taron tattaunawa da dattawa da masu ruwa da tsaki da matasa a karamar hukumar Abak ta jihar Akwa Ibom.
Ministan ya bayyana cewa tuni gwamnatin tarayya ta tsara hanyoyin da za a yi amfani da su wajen karya farashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin sauke farashin gas
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ya bayyana matakan da ma’aikatarsa ta dauka na rage tsadar iskar gas da kuma samar da iskar gas musamman ga kamfanonin da ke samar da wutar lantarki.
Ya tabbatar da cewa wannan yana cikin yunkurin gwamnatin tarayya na shirin kawo karshen tsadar kayayyakin da ake amfani da su a Najeriya.
Bayanin da ministan ya gabatar
“Za a iya cimma hakan ta hanyar kafa masana’antar iskar gas a sassa daban-daban na kasar nan, wanda a halin yanzu ma’aikatarmu na aiki akai kuma tana kira da mutane su karbi kudirin hannu biyu-biyu.
“Dalilin tashin farashin a halin yanzu shi ne fitarwa da shi da ake zuwa kasashen waje da kuma bukatar amfani da shi a cikin gida. 'Yan kasuwa na amfani da wannan damar suna sayar da shi da tsada.
- Ministan gas,
Ya kara da cewa suna aiki ba dare ba rana wajen ganin an samar da daidaitaccen tsarin farashin gas na dafa abinci a kan farashi mai rahusa, cewar jaridar Premium Times
Ya kuma tabbatar da cewa matakin da zasu dauka nan gaba shine dakatar da fitar da iskar gas, yana mai bata tabbaas kan idan aka dakatar da fitar da ita, farashin zai ragu.
Farashin gas ya kai N1,000
A wani rahoton kuma, kun ji cewa, 'yan Najeriya sun nuna rashin jin dadi da tashin farashin gas din girki, wanda aka ce ya kai kimanin N1,000 kan kowane kilo.
Hauwa Muhammed, wacce ke zama a Olodi-Apapa, ta ce ta cika da mamaki da jin sabon farashin na N1,000 a lokacin da ta je gidan mai.
Asali: Legit.ng