Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu Ya Rasu

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu Ya Rasu

  • Dr. Ogbonnaya Onu, tsohon gwamnan Abia kuma tsohon ministan kimiyya da fasaha a zamanin mulkin Buhari, ya rigamu gidan gaskiya
  • A cewar wata majiya ta kusa da marigayin, tsohon gwamnan ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a wani asibitin Abuja
  • A zaben 2023, marigayi Onu, ya tsaya takarar neman kujerar shugaban kasa na jam’iyyar APC amma ya sha kaye a hannun Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnan farar hula na farko na jihar Abia kuma tsohon ministan kimiyya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu, ya rasu.

Tsohon ministan Buhari, Ogbonnaya Onu ya rigamu gidan gaskiya
Wata majiya kusa da Onu ta ce tsohon gwamnan ya rasu ne bayan doguwar rashin lafiya. Hoto: @chief_paddy
Asali: Twitter

"Ya jima yana rashin lafiya" - Majiya

A cewar wata majiya ta kusa da marigayin da ta zanta da jaridar Tribune a ranar Alhamis, tsohon gwamnan ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a wani asibitin Najeriya.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin ‘yan uwan marigayin a Ebonyi wanda ya tabbatar da rasuwarsa ya ce iyalansa sun shirya kai shi kasar waje bayan hutun Sallah.

"Ya jima yana rashin lafiya kuma danginsa sun ce za su tafi da shi kasar waje domin samun kulawar kwararrun likitoci amma Ubangiji bai nufa zai kai lokacin ba."

- A cewar majiyar.

Onu ya zama gwamnan Abia na farko

Jaridar SaharaReporters ta ruwaito cewa abokansa da ‘yan uwan ​​sa sun yi dafifi a gidansa da ke Abuja tun bayan jin labarin domin yin ta’aziyya ga iyalansa.

Ogbonnaya Onu ya yi aikin koyarwa a sakandare da kuma jami’ar jihar Fatakwal, daga bisani ya shiga harkar siyasa a matsayin dan takarar kujerar sanata a tsohuwar Imo a jam’iyyar NPN.

Marigayin ya shiga jam'iyyar Republican Convention inda ya yi takarar gwamnan Abia a shekarar 1991 kuma Allah ya bashi nasara duk da kalubalen da ya fuskanta.

Kara karanta wannan

Ka daina sa baki: Kungiyar Arewa ta ja kunnen Kwankwaso saboda kalamansa

Onu ya yi takarar shugaban kasa

A watan Janairun 1992 aka rantsar da Onu a matsayin gwamnan Abia na farko, kuma shi ne shugaban kungiyar taron gwamnonin Najeriya na farko.

A shekarar 1999 ya samu tsayawa takarar shugaban kasa karshin jam'iyyar APP amma ya hakura ya bar mukamin ga Olu Falae bayan da PP ta ta hade da Alliance for Democracy.

A zaben 2023, marigayi Onu, mai shekaru 72 a duniya, ya tsaya takarar neman kujerar shugaban kasa a APC amma ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon dan majalisar wakilai ya rasu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon dan majalisar wakilai, Mohammed Ibrahim Idris ya rasu bayan dawowa daga masallacin Idi.

An ruwaito cewa Idris shi ne ɗan tsohon gwamnan jihar Kogi kuma ya yi wakilcin ne a lokacin mahaifinsa na kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.